1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron hukumar IAEA

March 7, 2006

ela, yayi barazanar hallaka, saban Praministan Palestinu Ismael Haniyeh.

A Kasar Kenya, dubunan mutane, sun shirya zanga zanga, domin maida martani, ga harin da dakarun gwamnati su ka kaiwa wata kafar sadarwa mai zaman kanta, a makon da ya gabata.

Yanzu ga labaran dalla dalla………………………………

Hukumar yaƙi da yaɗuwar makaman nuklea ta Majalisar Ɗinkin Dunia, ta shiga yini na 2, a zaman taron, da ta buɗa jiya a birnin Vienna.

Wakilan ƙasashe 35, membobin wannan hukuma, na tantana batutuwa daban daban, da su ka haɗa da matsalar makaman nukleyar ƙasar Iran, da ake ta famar kai ruwa rana, a kan ta, a halin yanzu.

A cikin wannan taro, wakilan za su binciki, rahotanin da shugaban hukumar, Mohamed El Baradei, ya tattaro, a game da rikicin na Iran, sannan su yanke shawara, a kan wajibcin gurfanar da Iran gaban komitin Sulhu na Majalisar Ɗinki Dunia, ko kuma akassin haka.

A nasu gefe, hukumomin Iran, sun jaddada matsayin su, na babu gudu babu ja da baya, a game da aniyar da su ka ɗauka, da sarrafa makamashin nuklea, domin ƙara samun wadatar hasken wurtar lantarki, a faɗin ƙasa.

Sannan sunyi, hannun ka mai sanda, ga Amurika ,da ke barazanar kai hari ga Iran, da cewar dakarun ƙasar, a shire su ke, su fuskanci ƙalubale ta ko wace hanya.