1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron hukumar MDD akan hakkin dan-Adam

March 14, 2005

A yau litinin hukumar MDD akan hakkin dan-Adam ta fara taronta na shekara a birnin Geneva

Tun misalin shekaru 50 da suka wuce ne aka kirkiro hukumar kare hakkin dan-Adam ta MDD domin ba da goyan baya da kuma sa ido akan manufofin girmama hakkin dan-Adam a sassa dabam-dabam na duniya. Hukumar ta kunshi kasashe 53 karkashin inuwarta, wadanda akan zabesu bisa tsari na shiyya. Amma kuma a daya bangaren hukumar na fama da matsalolin dake nema su kai mata iya wuya, kamar yadda aka ji daga bakin Claude-Adrien Zöller, kwararren masani akan hakkin dan-Adam a garin Geneva, inda ya kara da cewar:

Gwamnatoci ne ke yanke shawara, wadda galibi ba wata nagartacciyar shawara ba ce, kuma ba za a iya hukuntasu ba. An yi watsi da ainifin nagartaccen matakin da aka saba tu’ammali da shi a cikin shekaru na 1980. Dalili kuwa shi ne kasancewar gwamnatocin kasashen da lamarin ya shafa suna kyamar wannan tsari saboda tasirinsa wajen fallasa take-takensu dangane da hakkin dan-Adam. An fuskanci wata alkibla ce a yanzun inda kasashen ke neman yin tasiri su kansu a maimakon ba da goyan ga manufar girmama hakkin dan-Adam.

Hukumar kanta ta kunshi kasashe masu tarin yawa, wadanda suka yi kaurin suna wajen take hakkin dan-Adam, kamar dai Sudan da Zimbabwe da China da Rasha ko kuma Cuba. A shekarun baya-bayan nan an fara samun hadin kai tsakanin wadannan kasashe domin hana duk wata shawara ta yin Allah Waddai da su. A yanzu haka babu wata dama da gabatar da kudurorin Allah Waddai dangane da Chechniya ko China ko Zimbabwe. Wannan ba shakka mummunan ci gaba ne a cewar Kenneth Roth, darektan kungiyar kare hakkin dan-Adam ta "Human Rights Watch". Sai ya ci gaba da cewar:

Wannan zaman dai tamkar gwaji ne ga gaskiyar matsayin hukumar ta MDD. Matsalar dake akwai shi ne kasancewar da yawa daga cikin membobin hukumar suna ko oho da manufofinta tare da fatali da duk wani abin da ya shafi hakkin dan-Adam.

A saboda wannan dalilin ne mahalarta taron na bana suka tsayar da shawarar mayar da hankali kacokam akan matakan garambawul ga tsare-tsaren hukumar. An tanadar da kudurori kimanin 120, wadanda suka shafi kasashe a wawware da kuma wadanda suka suka jibanci al'amuran hukumart baki daya. Sai kuma rahotanni dabam-dabam da za a tattauna kansu kamar dai halin da ake ciki a Nepal da kuma matsayin hakkin dan-Adam a karkashin matakan murkushe ta’addanci na kasa da kasa.