1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron hukumar samar da abinci ta duniya kan Somaliya

July 25, 2011

Man'yan ƙungiyoyi na duniya na nazarin samar da hanyoyin magance bala'in yunwa da ya afkawa Somaliya

Mata da yara sun tagayara sakamakon fari a SomaliyaHoto: picture-alliance/dpa

mambobin hukumar abinci da ta aikin gona ta Majalisar Ɗinkin Duniya wato FAO sun ka gudanar da wani taro a birnin Rome na ƙasar Italiya da nufin gano hanyoyin warwware matsalar yunwa da ta afakwa wasu ƙasashe da ke kusurwar gabashin Afrika.

Shi dai wannan taron an gudanar da shi ne a ƙarƙashin jagorancin shugaban hukumar da kuma wakilan manbobin hukumar su ɗari da sha tara da ma dai hukumomi daban-daban na Majalisar Ɗinki Ɗuniya duka dai da nufin gano bakin zaren warwware bala'in yuwan da ya afkawa yankin na kusurwar gabashin Afrika.

Mahalarta taron dai sun baiyana cewar dole ne a ɗau mataki gaggawa kan matsalar domin gujewa dagulewar lamarin da ma dai bazuwar sa zuwa sauran ƙasahsen da ke kusurwar ta gabashin Afrika kazalika sun baiyana cewar yana da matuƙar muhimmanci a dafa wa waɗanda a halin yanzu ke fama da bala'in yunwa da ma dai abubuwan da su ka dogara kan su don samun abin kai wa bakin salati.

Kazalika sun baiyana cewar ya kyautu ƙasashen shidda da wannan matsala ta fi shafa su yi aiki kafaɗa da kafaɗa da juna domin kai wa ga nasara sannan kuma sun ambato cewar ƙofar bada taimako a buɗe ta ke ga duk wanda ke da muradin yin hakan musamman ma dai manoma da masunta da makiyaya waɗanda rayuwar su ta dogara kacokan kan waɗanan sana'o'i.

Da ta ke tofa albarkacin bakinta jim kaɗan bayan kammala taron Angela Hinrichs ta ƙungiyar abinci da noma ta Majalisar Ɗinkin Duniya cewa tai baya ga bala'in fari, matsaloli da dama sun taimaka wajen ta'azzarar matsalar.

''Ta ce mazauna yankin gabacin Afirka ƙananan manoma ne da su ka dogara kacokan a kan aikin noma ko kiwon dabbobi waɗanda wasu daga cikinsu ba sa zama waje ɗaya, sai dai su riƙa watangaririya daga wannan wurin zuwa wancan. Hatta a lokacin damina mai albarka a kan fuskanci ƙarancin abinci saboda bunƙasar yawan jama'a a cikin hamzarin da ake samu ta yadda abin da ake samarwa ba ya isa. Baya ga haka a kan yi kiwo fiye da ƙima ta yadda makiyayan sai sun haɗa da tafiya mai nisa wajen nemo abin da dabbobinsu za su yi kalaci da shi.''

Ita ma Josette Sheeran, daga ƙungiyar taimakon abinci ta Majalisar Ɗinkin Duniya, wadda ta kai ziyarar ganin ido a yankin a ƙarshen makon da ya gabata ta bayyana kaɗuwarta da halin da ake ciki a yankin .

''Ta ce na ga yara masu tarin yawa waɗanda ga alamu ba za su tsira daga wannan bala'in ba. Kazalika iyayen yara da dama da na tattauna da su sun baro 'ya'yansu a baya saboda ba za su iya ci gaba da goyon su ba. Ya zama wajibi a kan su su ɗauki wannan matakin saboda su ceci rayukansu ragowar 'ya'yan nasu. Akwai kuma yaran da su ka mutu a hannun iyayensu a kan hanya a fafutukar neman hayewa tudun tsira.''


Yayin wannan taron dai, bankin duniya ya bada gudummawar sama da dala miliyan ɗari biyar domin ceto yankunan da bala'in ya afkawa. Mafi akasarin kuɗin da bakin na duniya ya bayar dai zai karkata ne wajen taimakawa makiyaya yayin da dala miliyan sha biyu daga cikin kuɗin zai amfani da su wajen agazawa waɗanda wannan matsala ta shafa cikin gaggawa.Sai dai duk da irin wannan taimakon da ake bayarwa musamman ma dai an kuɗi Angela Hinrichs na ganin cewar sai an ƙra yin hoɓɓosa domin samun nasarar da aka sanya a gaba.

''Ta ce a halin da ake ciki yanzu wajibi ne a bada taimakon gaggawa, a lokaci guda kuma tilas ne a haɗa da taimako na tsawon lokaci domin tada komaɗar ayyukan noma yadda zai yi daidai da saukar damina ta yadda manoma za su samu iko noma gonakin su da kuma kare lafiyar dabbobinsu. Wajibi ne nan gaba a mayar da hankali sosai a kan harkar noma da ma kasuwancin amfanin da ake nomawa da kyautata hanyoyin sadarwa da tsarin noman rani da irin shuka ta yadda za a iya kauce wa irin wannan matsala nan gaba.''

Daga ƙasa za a iya sauraron sautin wannan rahoto tare kuma da rahoton da Abdullahi Tanko Bala ya shirya mana dangane da yadda hukumar ta abinci ta duniya ta shirya jigilar cimmaka zuwa ƙasar ta Somaliya bayan da ƙungiyar Al-shabaab ta sassauta haramcin da ta yiwa ƙungiyoyi masu kai agaji

Mawallafi : Ahmed Salisu
Edita : Abdourahamane Hassane



Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani