1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron hukumomin sadarwa na Afirka a Nijar

Abdoulaye Mamane AmadouJuly 23, 2015

Hukumomin koli na sadarwa na wasu kasashen Afrika, sun yi nazari kan yin adalci wajan baiwa 'yan takara damar shiga a kafafen yada labarai na gwamnati.

Hoto: AFP/Getty Images/A. Joe

A kalla dai hukumomin Koli na sadarwa na kasashen 13 ne suka halarci zaman taron da ya gudana a birnin Yamai na Jamhuriyar Nijar. A wani mataki na kwatanta adalci da shinfida gaskiya a yayin da ake cikin yanayi na zabe tsakanin 'yan takara a fannin shiga kafofin yada labarai na gwamnati da akasari masu rike da mulki ke mamaye komai, tare da yin abun da suke so a lokuttan yakin neman zabe. Da yake tsokaci kan wannan batu, shugaban babbar hukumar koli ta sadarwa ta kasashen na Afirka Abdourahmane Ousmane wanda shi ne shugaban hukumar sadarwa ta Jamhuriyar Nijar, ya ce idan har ana so a kawo karshen iri-irin wannan matsala, sai fa hukumomin sadarwa sun zage damtse.

Babban kalubale a gaban hukumomin sadarwa na Afirka

Hoto: DW/Bilderbox.com


Wadanda suka yi zabe a kasashensu, sai su sanar da mu yadda suka yi nasu tsarin shinfida adalci, kenan idan na su tsarin ya gamsar sai wadanda za su yi zabe nan gaba su yi koyi da na su tsarin saanan kuma su bayyana muna matsalolin da suka fuskanta lokacin da suka yi nasu zaben don masu yi nan gaba su kauce musu.

Bisa ga ga laakari da manya-manyan kalubalen da ke gaban hukumomin sadarwar na afrika, babban taron nasu ya tsayar da wasu muhimman matakkai wadanda yake ganin na iya kawo masalaha cikin koke-koken da al'umma ke yi da su.
Mme Nathaly Some shugabar hukumar sadarwa ce ta kasar Burkina Faso, ta yi tsokaci kan irin amfanin da kasarta za ta samu daga wannan zaman taro ganin irin yadda suma suke cikin shirye-shiryen zaben da zai gudana nan da 'yan watanni masu zuwa.

Hoto: DW

Masu mulki na mamaye kafofin yada labarai a Afirka

Duk inda ake musayar raayi na kara wa juna sani kan batun tafiyar da ayyukanmu na hukumar koli ta sadarwa, to mu na kokarin halarta don tunkarar hukumomin sadarwar takwarorinmu na kasashe, sabo da haka ne ma ya sa mu ka halarci wannan taron na kasar Nijar domin mu a Burkina Faso, a bana ne kawai muka fara shiga cikin wani yanayi na shirya zabubuka a cikin tsarin wata gwamnati ta rikon kwarya, don haka mun zo ne domin samun bayyanai kan hanyoyin da sauran kasashe suka bi mu ma mu yi koyi.

Hukumomin dai na sadarwa na kasashen 13 na Afirka, sun ce za su yi amfani da tsarin da kasar Togo ta yi a zabenta na watan Afrilun wannan shekarar ta hanyar daidaita shugaban kasar da sauran 'yan takarar da ke hamayya da shi daga ranar da aka ce an kaddamar da yakin neman zabe. Sai dai wasu masu sharhi na ganin cewa, ko da dai hakan za ta faru, sai dai a wasu kasashen ba dai Nijar ba, domin kuwa a Nijar munduwar da ke zagaye da masu iko tafi karfin wuyan hannun hukumar ta koli ta sadarwa ta CSC.