1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Taron inganta harkokin kasuwanci a Afirka

Mouhamadou Awal Balarabe Kossivi Tiassou/SB
April 16, 2025

Ana taron kasashen Afirka a birnin Kinshasa na Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango domin gaggauta aiwatar da tsarin yarjejeniyar ciniki maras shinge tsakanin kasashen nahiyar da aka amince tun shekarun da suka gabata.

AfCFTA
Tahsar jiragen ruwan Kenya karkashin yarjejeniyar AfCFTAHoto: Xinhua News Agency/picture alliance

Kasashen Afirka na gudanar da taro a birnin Kinshasa na Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango domin gaggauta aiwatar da tsarin ciniki maras shinge tsakaninsu da aka fi sani da "Zlecaf"(French) ko AfCFTA (English). Sai dai bayan shekaru bakwai da sanya hannu kan yarjejeniyar ta cinikayya, kasashen Afirka na ci gaba da fuskantar kalubale wajen cimma burin da aka sa a gaba.

Babban burin da tsarin Zlecaf ko AfCFTA ya sa gaba tun bayan amincewa da shi a watan Maris na 2018, shi ne karfafa kasuwanci a tsakanin kasashen Afirka, musamman ta hanyar samun zirga-zirgar kayayyaki da jari da kuma shige da fice na 'ya'yan wannan nahiya ba tare da tsangwama ba. Sai dai wannan na zama kalubale ga nahiyar, saboda har yanzu cinikin tsakanin Afirka bai fi kashi 15% ba, alhali idan aka kwatanta da wasu yankuna, ciniki ya kai kashi 70% a tsakanin kasashen Turai yayin da ya kai kashi 50% a Asiya. Saboda haka ne taron Kinshasa da ke zama wani muhimmin mataki na tabbatar da burin runbaya cinikayya a Afirka.

Karin Bayani: Cinikayya mara shinge ta kafu a Afirka

AfCFTAHoto: Ghana Presidency/Xinhua News Agency/picture alliance

Sai dai, shekaru bakwai bayan amincewa da Zlecaf ko AfCFTA, kasashe takwas ne kawai ne suka fara aiwatar da yarjejeniyar a matsayin gwaji, ciki har da Ghana da Tunisiya da Kenya da kuma Ruwanda. Amma Mounirou Alioune Kane, jami'in gudanar da bincike a cibiyar kasuwanci da hada kai da ci gaban Afirka (ENDA-CACID) da ke birnin Dakar na kasar Senegal, ya ce wannan ba wani abin mamaki ba ne duba da jadawalin Zlecaf.

Wata sarkakiya da kasashen na Afirka ke fuskanta, ita ce rashin isasshen tallafi daga kamfanoni masu zaman kansu, lamarin da ke sa shirin ciniki na bai daya ci gaba da tafiyar hawainiya. Wannan ne ma dalilin da ya sa sakatariyar Zlecaf mai hedkwata a Ghana, ta kaddamar da hanyoyin shawo kan matsalolin. A halin yanzu dai, an riga an yi musayar kayayyaki ko hajoji 96 a matsayin gwajin dafi, inda kashi 90% daga ciki suka cika ka'idodi. Amma shingayen da ba su da alaka da kudin fito na  kwastam na ci gaba da kawo cikas ga kasuwancin kasa da kasa.

Yarjejeniyar kasuwancin a nahiyoyin duniya

A lokacin da ake maganar dunkulewa a bangaren tattalin arzikin Afirka, wani abu da ke zama karfen kafa shi ne shawarar da kasashe uku mambobin kungiyar ECOWAS, Mali, Burkina Faso da Nijar, suka yanke na ficewa daga kungiyar, inda suka kafa tsarin ciniki na kansu.

A daidai lokacin da Afirka ke fadi tashin hada karfi da karfe a fannin kasuwanci, sabon rikicin kasuwanci da shugaban Amurka Donald Trump dai ya kaddamar na kara harajin fito ya kawo cikas ga saye da sayarwa a duniya, lamarin da ka iya mummunan tasiri ga burin Afirka na cinikin bai daya.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani