1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Babban taron jam'iyyar adawa ta ADC a Najeriya

Uwais Abubakar Idris
April 14, 2026

Jam'iyyar adawa ta ADC ta gudanar da babban taronta a Abuja inda 'yan jam'iyyar daga jihohin Najeriya suka hallara tare da jiga-jigan jam'iyyar. Taron da ya yi armashi saboda shi ne irinsa na farko.

Taron jam'yar adawa ta ADC a birnin Abuja na Najeriya
Taron jam'yar adawa ta ADC a birnin Abuja na NajeriyaHoto: Uwaisu Abubakar Idris/DW

Wannan taro na jamiyyar ADC da ya dauki hakali sosai saboda shine na daura damba ga yayyan jamiyyar da suka lashi bakin takobi na sai sun gudanar da shi duk da tirka-tirkar da aka fuskanta kan samun uzurin da za a gudanar da taron, wanda sai a maraicen ranar litini suka samu wajen shakatawa na Rainbow da ke a birnin Abuja.

Mahalarta taron

Taron jam'yar adawa ta ADC a birnin Abuja na NajeriyaHoto: Uwaisu Abubakar Idris/DW

Wannan ya sanya taron ya kara armashi da daukan hakalin 'yan jam'iyyar. Barrister Solomon Dalung jigo ne a jamiyyar ta ADC wanda ya nuna gamsuwa da taron.

Shiga wurin da aka gudanar da taron dai ya zama jan aiki koda ga wadanda ke da katin izinin shiga saboda tsanain yawan jama’a. Inda jam'iyyar ta buge da amfani da jami’an tsaron da ta yi haya don hada da kalilan da hukuma ta ba su.

Shugaban jamiyyar David Mark da aka baiwa ragamar tafiyar da jam'iyyar ya bayyana cewa samun gudanar da taron na da matukar muhimmanci ga wanzuwar dimukurudiyyar Najeriya. Amma mene ne hallacin taron nasu sanin cewa hukumar zabe ta yi masu kashedi? Naomi Lasara it ace shugabar mata ta jamiyyar ADC wadda ta ce jam'iyyar za ta bunkasa ta yi tasiri a zabukan Najeriya.

Sauran wakilai

Taron jam'yar adawa ta ADC a birnin Abuja na NajeriyaHoto: Uwaisu Abubakar Idris/DW

Akwai dai wakilai da suka wo taka daga daukacin jihohin Najeriya ciki har da Hajiya Ma’am Kyari jihar Borno inda daya daga cikin wakilan da suka hallarci taron kuma ta ce an smau abin da ake bukata.

An dai kai ga yanke wuta a wurin da suka yi taron a dai dai lokacin da ake shirin gudanar da shi abin da ya sanya Dr Yunusa Tanko na hannun daman Peter Obi ne daya daga cikin jiga-jigan a jam'iyyar ta ADC da ke maraba da matakan da ake dauka.

Har zuwa wannan lokaci 'yan jam'iyyar da can suna gudanar da taron nasu inda za su tabbatar da ragamar jam'iyyar ga sabbin shugabanin da mafi yawa za a yi tsarin cimma yarjejeniya ne ba zabe ba.