Taron jamiyyar adawa ta NLD a Birma
March 8, 2013Jamiyyar adawar Birma ta Aung San Suu kyi ta buɗe taron ƙolin ta mai cike da tarihi wanda ake ganinsa a matsayin wata dama na bunƙasa jamiyyar wadda duk da cewa tana da farin jini, bata gama ƙwarewa a fagen siyasa ba, kuma a yanzu haka tana fuskantar ƙalubale a cikin gida gabannin babban zaɓen ƙasar da ake sa ran yi a shekarar 2015 idan Allah ya kai mu.
To sai dai masana sun fara sanya alamar tambaya kan ko jamiyyar ta NLD na da ƙarfin tinkarar irin ƙarin ƙalubalen da zata fuskanta wajen tsayawa takara a wannan ƙasar da ke fama da koma bayan tattalin arziƙi wacce kuma kusan duk cibiyoyin samar da abubuwan more rayuwarta sun durƙushe.
Aƙalla wakilai 850 ke halartar wannan taron na wuni uku wanda zai gudanar da sauye-sauye a tsarin shugabancin jamiyyar ya kuma tsara irin matakan da zata ɗauka nan gaba musamman wajen cimma burinta na karɓar ragamar mulkin ƙasar.
Mawallafiya: Pinaɗo Abdu Waba
Edita: Zainab Mohammed Abubakar