Taron kafofin yada labarun duniya da DW ke shiryawa
July 3, 2014![GMF Global Media Forum 2014](https://static.dw.com/image/17746605_800.webp)
Talla
Mutane kimanin 2000 daga kasashe 100 da suka fito daga bangarorin rayuwa daban-daban kamar na kafofin yada labaru da 'yan siyasa da 'yan kasuwa da kuma masu ilimin jami'a, sun kwashe tsawon kwanaki uku suna tattaunawa tare da tabka muhawarori game da kalubalen da duniya ke fuskanta na ci gaba, da muhimmiyar rawar da jarida ke takawa a ciki.