Taron kare muhalli a tsibirin Bali
December 4, 2007Talla
Masu fafatukar kare muhalli dake halartar taron ƙolin da Majalisar Ɗinkin Duniya ta shirya kan sauyin yanayi a tsibirin Bali na ƙasar Indonesia sun zargi kasashe masu arziki da rashin tallafawa kasashe matalauta waɗanda ke fama da bala´o´i kamar ambaliyar ruwa, fari sakamakon ɗumamar doron ƙasa. Babban taron na kwanaki 11 wanda ke samun halarcin wakilai kimanin dubu 10 daga ƙasashe 190 shi ne irinsa mafi girma da aka taba shiryawa da nufin share fagen yin wata tattaunawa dangane da wata yarjejeniyar kare muhalli wadda zata maye gurbin ta birnin Kyoto da ke kare aiki a cikin shekara ta 2012. Sabon Firaministan Australiya Kevin Rudd ya sanya hanu kan yarjejeniyar a matakin farko na kama aiki. Kasar Amirka ce kaɗai daga cikin kasashe mafiya arzikin masana´antu da ba ta albarkacin yarjejeniyar ta Kyoto ba.