1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaIsra'ila

Taron G7 zai tattauna sammacin kama Benjamin Netanyahu

Abdourahamane Hassane
November 22, 2024

Ministocin harkokin waje na kasashe masu ci gaban masanantu G7 za su yi taro a ranaikun Litinin da Talata a kusa da birnin Roma na Italiya,

Hoto: Ciro De Luca/REUTERS

 Ministocinza su  tattauna kan sammacin kama Benjamin Netanyahu da Mohammed Deif na Hamas  da kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ta bayar, kamar yadda firaministan Italiya Giorgia Meloni ta sanar. Wannan sanarwa na zuwa ne, bayan maganganu masu cin karo da juna daga ministoci guda biyu na firaministar. Yayin da Ministan Tsaro Guido Crosetto ya tabbatar da cewa Italiya za ta  kama Netanyahu da ministansa na tsaro  Gallant idan sun zo Italiyar. Mataimakin firaministan kasar Matteo Salvini, na jam'iyyar masu adawa da 'yan cirani kuma abokan kawance na gwamnatin, ya ce suna  yin maraba da Netanyahu idan ya zo  Italiya.