Taron kasashe aminan Siriya a birnin Istanbul
April 1, 2012Kasashen yammacin Turai da na Larabawa sun amince da majalisar kasa ta Siriya wadda yan adawa suka kafa a matsayin halastacciyar majalisa ta al'ummar Siriya. Rukunin kasashe 83 da suka halarci taron aminan Siriya da ya gudana a birnin Santanbul na kasar Turkiya sun ce za'a auna martabar shugaba Bashar al-Assad ne da abin da ya aikata amma ba yawan alkawura ba musamman game da kudirorin nan shida na wanzar da zaman lafiya da Kofi Annan ya gabatar. A waje guda tarzomar da ta wakana a sassan kasar Siriyar a yau ta yi sanadiyar mutuwar akalla mutane 40 a cewar masu sa ido dake nazarin al'amuran dake faruwa a kasar. A hannu daya dai kasashen China da Rasha da kuma Iran sun kauracewa taron na Istanbul. Ministan harkokin wajen Turkiya Ahmet Davutoglu ya kwatanta halin da ake ciki a Siriya da abin da ya faru a Bosnia a shekarun 1990.
Mawallafi: Abdullahi Tanko Bala
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe