1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaFaransa

Kasashe na taro kan karfafa amfani da nukiliya

September 28, 2023

Akalla ministocin kasashen duniya 15 za su fara taro a birnin Paris na Faransa da nufin gaggauta dawo da makamashin nukiliya da kuma karfafa gwiwar samar da kudade don girka cibiyoyin kasa da kasa masu amfani da shi.

Türkei Kernkraftwerk Akkuyu
Hoto: Akkuyu Nuclear/Tass/dpa/picture alliance

Ana sa ran jami'ai da masana'antun sarrafa makamashin daga Japan da Kanada da Amurka da Burtaniya da kuma wasu kasashen Tarayyar Turai za su halarci taron na kwanaki biyu da za a fara a ranar Alhamis (28.09.2023).

Karin bayani: Jamus za ta dadakar da cibiyoyin makamashi uku

Babban burin taron dai shi ne ayyana taswirar hanyoyin sake kaddamar da makamashin nukiliya a fadin duniya, abin da zai taimaka wajen cimma manufa ta yin bankwana da gurbataccen hayaki na Carbone da kuma karfafa wadatar makamashi.

Karin bayani: Rasha za ta gina wa Masar tashar nukiliya

Gabanin taron na Paris, shugaban hukumar makamashin nukiliya ta duniya IAEA ya ce ya yi imanin da cewa nukiliya wata hanya ce da ya kama a karfafa wajen samar da makamashi mai inganci wanda zai wadaci duniya.