1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron kasashen kungiyar EU da na kasashen yankin Tekun Bahar Rum.

Mohammad Nasiru AwalDecember 1, 2003
A bana an gaiyaci kasar Libya ta halarci wannan taro a matsayin ´yar kallo. Bayan da MDD ta dage takunkumin da ta sanyawa wannan kasa, kuma aka cimma daidaito game da diyyar da za´a ba wadanda ayyukan tarzomar Libya suka rutsa da su, yanzu kungiyar tarayyar Turai EU ta kuduri aniyar inganta dangantakarta da wannan kasa ta arewacin Afirka. A ma halin da ake ciki huldodin cinikayya tsakanin kasashen EU da Libya sun inganta, inda Libya din ke sayarwa kasar Italiya kashi 50 cikin 100 na yawan mai da Italiya din ke bukata, sannan Jamus kuma ke sayen kashi 13 cikin 100 na danyen mai da take bukata a shekara.
Italiya dai na da sha´awar inganta huldodin diplomasiyya da Libya, musamman don gano bakin zaren magance matsalar dubban ´yan gudun hijirar Afirka, wadanda ke bi ta tekun Bahar Rum a yankin Libya don shiga wasu yankuna na Italiya. Haka zalika kungiyar EU ta shafe shekaru da dama tana kokarin cimma wata yarjejeniya da kasashen Aljeriya, Marokko da Turkiya don samun saukin mayar da ´yan gudun hijirar kasashensu, amma har yau hakan ba ta samu ba, domin wadannan kasashen ba su da wata sha´awar yin haka din.
A halin da ake ciki kungiyar ta cimma wata yarjejeniyar ciniki wadda ta tanadi bude kan iyakokinta ga kayakin kasashen Marokko, Tunisia, Isra´ila, Jordan da kuma Turkiya. Ko da yake an kammala tattauna batun kulla irin wannan yarjejeniyar da kasashen Aljeriya da Masar, amma har yanzu ba ta fara aiki ba. Yayin da kasar Libanon da yankunan cin gashin kai na Falasdinu kuma ke kara nuna sha´awar shiga cikin wannan yarjejeniya.
Su kuwa kasashen Malta, Cprus da Turkiya, da ma suna cikin wata tarayya ta kawad da shingayen ciniki da kungiyar EU, musamman kasancewar su suna daga cikin jerin kasashen da za´a dauka cikin kungiyar ta EU.
Manufar wannan yarjejeniya ta hadin kan cinikaiya ita ce taimkawa harkokin cinikaiya maras shinge tsakanin kasashen yankin Tekun Bahar Rum. An jiyo kwamishinan dake kula hulda da kasashen kasashen ketare na kungiyar EU Chris Patten na cewa tsakanin shekara ta 2000 da ta 2006 kungiyar EU ta ware makudan kudade sama da EURO miliyan dubu 5 don taimakawa a inganta harkokin cinikaiya da na tattalin arziki a kasashen yankin na Tekun Bahar Rum.
Ita kuwa kungiyar EU na bukatar kasashen yankin da su aiwatar da canje-canje ne na siyasa, tattalin arziki tare da inganta matakan kare hakin dan Adam.