Taron kasashen tarayyar Turai da na bakin tekun Bahar Rum
November 27, 2005Talla
Jim kadan gabanin a fara taron kolin kasashen kungiyar tarayyar Turai da takwarorinsu na yankin tekun Bahar Rum, MDD ta yi kira da a kara ba da kariya ga ´yan gudun hijira daga Afirka. Wata mai magana da yawun hukumar taimakawa ´yan gudun hijira ta MDD ta yi zargin cewa sau da yawa ana daukar ´yan gudun hijirar tamkar bakin haure. Muhimman batutuwan da za su dauki hankali a taron kolin na yini biyu da za´a fara yau lahadi a birnin Barcelona na kasar Spain sun hada da na ´yan gudun hijira da yaki da ´yan ta´adda da kuma shirye shiryen kirkiro wani yankin ciniki maras shinge. Sabuwar shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel na daga cikin shugabannin tarayyar Turai da zasu halarci taron kolin.