1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Taron kasashen Turai da China

Suleiman Babayo ZMA
December 7, 2023

Taro tsakanin kungiyar kasashen Turai da China a birnin Beijing na kasra ta China ya mayar da hankali kan batutuwan da suka shafi kasuwanci da dinke barakar da ke tsakanin bangarorin biyu.

China | Taron kasashen Turai da China
Taron kasashen Turai da ChinaHoto: Pignatelli/EUC/ROPI/picture alliance

Shugabar hukumar Tarayyar Turai Ursula von der Leyen ta shaida wa Shugaba Xi Jinping na kasar China cewa ya dace bangarorin biyu da suke da cinikayya mafi girma su dinke barakar da ke tsakaninsu. Shugabar ta bayyana haka lokaci taro karo na farko na keke-da-keke tsakanin shugabannin kungiyar kasashen ta Turai da China cikin shekaru hudu.

Bangarorin na China da Turai suna kuma neman hanyoyin gyara dangantakar diflomasiyya da ta yi tsami.

Anasa bangaren Shugaba Xi Jinping na China ya yi gargadi bai dace Turai da China su dauki juna a matsayin abokan gaba ba, ko kuma yin fito na fito da juna saboda sabanin tsarin siyasa, inda ya kara da cewa ya dace duk bangarorin su yi aikin tare domin samun ci-gaba. Yanzu haka ana ci gaba da gudanar da taron a birnin Beijing na China.