Taron kawayen Ukraine
October 5, 2023Shugabannin da ke halartan taro karkashen wata kungiya da suka kira European Community Forum wace aka kafa watan Febrairu bayan da Rasha ta kaddamar da hari kan Ukraine, an kafa ta domin duba makomar tsaron Turai. Duk da cewa kungiyar na bada goyon bayan kudi da makamai ga Ukraine, amma kawo yanzu Ukraine ta gaza girgiza Rasha daga yankunan da Rasha ta mamaye. A cewar masharhanta, hadin kan kasashen na Yamma wajen taimakawa Ukraine yana fara samu babbar baraka, musamman daga cikin gidan kasashe irinsu Amirka da Jamus da sauransu. Ko da a safiyar wannan Alhamis, wata mijiya daga fadar gwamnnatin Jamus ta sanar da cewa shugaban gwamnati Olaf Schulz ba zai mika wa Ukraine, makamai masu linzami kirar Jamus da Ukraine ke ta neman a aika mata ba. Jami'in ya ce za a duba batun amma sai wani lokaci nan gaba.