1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron shawo kan kalubalen da kasar ke fuskantar Mali

Abdoulaye Mamane Amadou GAT
December 16, 2019

Gwamnatin kasar Mali ta bude wani taron koli na kasa da zummar samar da hanyoyin shawo kan matsalolin zamantakewa da kasar ke fuskanta da ke da nasaba da ayyukan kungiyoyin 'yan ta'adda da kuma rikicin kabilanci.

Militär Konferenz Mali
Hoto: Reuters

A kasar Mali a karshen makon da ya gabata ne aka bude zaman taron koli na kasa shawo kan matsalolin kasar. Taron wanda ya samu halartar wakilan gwamnati da na bangarori dabam-dabam na al'ummar kasar na da burin samar da mafita ga matsalolin da suka dabaibaye kasar da suka hada da na ta'addanci da kabilanci da ma na 'yan tawaye da ke neman ballewa daga yankin arewacin kasar.


Tun daga farko dai an shafe tsawon lokaci ana hasashen cewa hadaddiyar kungiyar 'yan awaren kasar Mali CMA ba za ta halarci taron ba. Sai dai kungiyar ta yi wa jama'a 'yar ba zata inda ta kasance a yayin babban taron da zai shafe tsawon kwanaki takwas ana tattaunawa kan matsalolin da ke addabar kasar Mali. Ko da yake a cewar wasu rahotanni, halartar kungiyar ta 'yan tawayen Abzinawan na zuwa ne da sharadi musamman ma game da batun kawo sauyi ga yarjejeniyar da ta cimma da bangaren gwamnatin kasar a birnin Alger na kasar Aljeriya.  Aliou Ag Mohamed shi ne kakakkin kungiyar cewa ya yi:

Hoto: DW/R. Guezodje


‘’Muna da cikakken fata ga wannan babban taron na tattaunawa, muna kuma fatan zai kasance taro ne da za a iya fede biri har wutsiya game da matsalolin da ke addabar Mali a cikin natsuya daga mahalartansa. Sai dai muna hasashen cewa taron na yanzu ba zai yanke hukuncin sake waiwayen yarjejeniyar da muka cimma da gwamnati ba ta zaman lafiya. Fatanmu shi ne 'yan Mali da ba su fahinci abin da yarjejeniyar ta kunsa ba da su ba mu dama mu fayyace masu abin da take ciki a yayin wannan taro.‘’


Sai dai ana taron ne ba tare da halatar wani bangare na jam'iyyun 'yan adawar kasar ba, inda madugun 'yan adawar kasar Sumaila Cissse ya zargi taron da zaman wani na shan shayi kawai da ba zai iya kai ga warware matsalolin da 'yan kasar ta Mali suke ciki ba. Matakin da gwamnatin kasar ta Mali ta koka da shi. sai dai har gobe kofofin taron na bude ga 'yan adawa in ji ministan sadarwa kuma kakakkin gwamnatin Mali Yaya Sangaré:

Hoto: Reuters/M. Konate


‘’Duk da mika hannu ga 'yan adawa da shugaban kasa da kwamiti na musamman na dattijawa suka yi 'yan adawa na ci gaba da fatali da wannan taron, suna masu cewa tuni sun san inda aka dosa tun a gabanin babban taron. To amma a dabra da haka kamata ya yi mu aminta da shiga taron kana mu bayar da yarda ga matakan da zai samarwa domin sake dora dan ba na tafiyar kasar nan sai da yarda.‘’


Wani abin da ke zaman tamkar gamo na katar a yayin taron shi ne ana soma taron kana kuma tsohon shugaban kasar Amadou Toumani Toure ya sake komawa a gida da zama baki daya, bayan ya shafe tsawon lokaci yana gudun hijira a Dakar babban birnin kasar Senegal. Ko da yake magoya bayansa sun ce dawowarsa a gida ba ta da nasaba ko daya da yadda ake gudanar da babban taron na kasar Mali.
Za a ci gaba da gudanar da taron dai har izuwa ranar 22 ga wannan watan a wani yunkuri na samun hadin kan bangarorin kasar da ba sa jituwa domin warware takaddamar a cikin ruwan sanyi kafin tunkarar wata matsalar ta daban da ke neman zamewa kasar karfen kafa.