1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron koli tsakanin kasashen EU da kasar China

February 14, 2012

Halin da Turai take ciki na rikicin kudi da batun dangantaka kan alal'amuran duniya suna daga cikin al'amuran da za'a duba a lokacin ganawar

China's Premier Wen Jiabao (C) poses with European Council President Herman Van Rompuy (L) and European Commission President Jose Manuel Barroso after they met in the Great Hall of the People in Beijing February 14, 2012. China and the European Union began their summit meeting in Beijing today, after it was postponed from last December. It will bring together Premier Wen Jiabao and President Hu Jintao with European Commission President Jose Manuel Barroso and European Council President Herman Van Rompuy. Premier Wen said recently that China has a stake in helping Euro zone countries get through their debt crisis, adding that Beijing was considering increasing its participation in rescue funds to address the European debt crisis. REUTERS/David Gray (CHINA - Tags: POLITICS BUSINESS TPX IMAGES OF THE DAY)
EU-China-Gipfel in Peking ChinaHoto: Reuters

Tun daga ranar Talata, wakilan kungiyar hadin kan Turai suka fara taron koli na hadin gwiwa na tuntubar juna karo na goma sha hudu tare da kasar China. Taron ana gudanar dashi ne a wani lokaci mai matukar wahala.Tun da farko wakila na Chjina da takwarorin su na kungiyar hadin kan Turai a watan Oktober na bara aka shirya yin sa a garin Tianjin , to amma kungiyar hadin kan han Turai ta dakatar dashi, saboda rikicin kudi da dimbin bashin dake kan Girka bai baiwa yan siyasar na Turai damar kai ziyara wani wuri ba.

Batun rikicin dimbin bashin dake kan kasashen Turai ana sa ran zai kasance a jerin al'amuran da za'a duba a lokacin taron kolin a China, idan Pirayim ministan na China, Wen Jiabao ya sadu da shugaban majalisar kungiyar hadin kan Turai, Herman van Rompuy da kuma shugaban hukumar kuingiyar ta hadin kan Turai, Jose Manuel Barosso. Musamman hakan ya zama wajibi ganin cewar China yanzu haka tana da hannayen jarin kasashen Turai na misalin dollar miliyan dubu har sau dubu ukku a hannun tana. Tun ma a lokacin ziyarar ziyarar dfa shugaban gwamnatin Jamus, Angela Merkel ta kai Peking a farkon watan Fabrairu Pirayim ministan na China yaki yarda a ja hankalin sa yayi wani karin alkawari na taimakon kasashen Turai, fiye da wanda kasar tayi a da can game da shiga matakan ceto kudin Euro. Maimakon haka, Pirayim minista Wen an ji yana cewa:

"Hanyar shawo kan matsalar dimbin bashin dake kan kasashen na Turai, tana tattare ne da kokarin da kasashen nahiyar zasu yi da kansu. China tana goyon bayan wannan kokari, kuma tana nazari game da asusun musamman da kasashen na Turai suka kafa domin ceto kasashe masu fama da dimbin bashi a kansu, wato asusun EFSF, ko kuma asusun hana fadi-tashin kudin na Euro wadanda burin su shine su taimaka domin shawo kan wannan rikici."

China da Turai suna da kusancin dangantakar tattalin arziki tsakanin su. A shekara ta 2010, bangarorin biyu sun yi musayar kayaiyaki ne adadin kudi Euro miliyan dubu 400 tsakanin su, abin da ya maida kungiyar hadin kan Turai ta zama mafi muhimmanci a bangaren ciniki da China. A daya hannun kuma, China kadan ya rage ta maye gurbin Amerika a matsayin kasa mafi muhimmanci a fannin cinikin kungiyar hadin kan Turai. Saboda haka ne Chinan take da matukar sha'awar samun nahiyar Turai mai koshin lafiya.

Tutocin China da na Kungiyar Hadin kan TuraiHoto: picture-alliance / dpa

Sai dai kuma ko da shike China ana iya kiran ta gagarumar kasa a fannin tattalin arziki, amma a bangaren siyasa kasar bata da karfi sosai. Duk da haka China din ta nunarda matsayin ta na siyasa a baya-bayan nan a kwamitin sulhuna majalisar dinkin duniya, lokacin da ta hau kujerar naki domin hana wucewar wani kudiri kan kasar Syria. A lokacin taron na wannan karo, kasar ta China da kungiyar hadin kan Turai zasu duba al'amuran da suka shafi yankuna dabam dabam, kamar dai misali, al'amarin nan mai wahala tattare da yadda zasu yi da kasar Iran.

Shugaban majalisar kungiyar hadin kan Turai, Herman van Rompuy yace banbancin ra'ayi tsakanin su ba wani sabon abu bane.

"Muna magana a fili tattare da banbancin dake tsakanin mu. Wannan ba wani boyayyen abu bane. Muna da kyakkyawar dangantaka da China, kuma muna kwatanta kanmu a matsayin abokan hadin gwiwa na hakika, to amma wajibine mu fitowa junan mu da gaskiya. Mun banbanta sosai a fannoni masu yawa, amma mun kuma daidaita a al'amura da dama. Muna da karfin zuciyar ci gaba da ganin dangantakar dake tsakanin mu ta ci gaba da kyawun da aka santa dashi."

Herman van Rompuy da masu masaukin saHoto: AP

A zahiri kuwa ba'a karancin al'amuran da bangarorin biyu suke da banbancin ra'ayi a tsakanin su. China tana bukatar a amince da ita a matsayin mai bin tafarkin jari hujja, a kawo karshen takunkumin hana sayar mata da makamai. Su kuma kasashen Turai ba suna kusantar China ne saboda rikicin Euro dake addabar su a yanzu kadai ba, amma suna bukatar hadin kanta a fannin kare muhalli da neman ta kara bude kasuwanncin ta ga kayaiyakin su da ganin China din ta kyautata manufofin ta na kare hakkin yan Adam.