Taron kolin EU da Afrika a birnin Luanda
November 24, 2025
Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron da shugaban gwamnatin Jamus Friedrich Merz da na Kenya William Ruto na daga cikin gomman shugabannin Turai da na Afirka da ake sa ran za su hallara a Luanda domin taron a daidai lokacin da wani sabon rashin jituwa ya kunno kai tsakanin Amurka da tarayyar Turai game da shirin Washington na kawo karshen yakin Ukraine.
Tattaunawar da kasashen Afirka za ta mayar da hankali ne kan batun cinikayya da 'yan gudun hijira da kuma ma'adanai da ake matukar bukata.
Shugaban gwamnatin Jamus Friedrich Merz ya ce shugaban Amurka Donald Trump ya shaida masa cewa a shirye yake ya hada hannu da tarayyar Turai wajen aiwatar da shirin zaman lafiya a Ukraine.
Merz ya ce Trump ya baiyana masa hakan ne a yayin tattaunawar da ya yi da shi a makon da ya gabata. Ya ce wannan shine abin da wakilan Ukraine da na Amurka da kuma na tarayyar Turai suka cimma a Geneva.
Ya yi wannan bayanin ne a daura da taron kolin EU da Afirka da ke gudana a Luanda.