1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron kolin kasashen musulmi da na Larabawa

Mahmud Yaya Azare
November 12, 2024

Taron koli na hadin gwiwar kasashen Larabawa da kasashen Musulmin duniya a babban birnin Saudiya Riyadh

Saudi-Arabien | Gipfeltreffen der Organisation für Islamische Zusammenarbeit und der Arabischen Liga in Riad
Hoto: ANKA

Taron na bana da ke zuwa bayan cika shekara guda da gabatar da makamancinsa bara a birnin Riyadh na kasar Saudiya inda kamar sauran tarukan larabawa ya takaita kawai ga yin tir da hare haren Isra'ila kan zirin Gaza. A wannan karon, bayan kisan da Isra'ila ta kwashe shekara guda tana yi wa Falalsdinawa da ya kai ga halaka kimanin mutane dubu 45 galibinsu yara kanana da mata da tsofi, bayan kwashe watanni kusan hudu tana ragarazar kasar Labanon da halaka fararen hula kimanin 5000. Taron hadin gwiwar da ya sami halartar galibin shuwagabanin Larabawa dana kasashen musulmi, ya zama wani dandalin caccakar juna kan zamansu kamar yadda firaim ministan Iraki, Muhammad Al sudany ya siffanta da taron ayya.

Karin Bayani: Kasashen Larabwa da na musulmi sun bukaci gaggauta tsagaita wuta a Gaza

Hoto: Turkish Presidency/Murat Kula/Anadolu/picture alliance

"Ya ce zan fadi gaskiya karara komin dacinta. Abin da muke bukata a yau ba shirya taruka bane da mu kanmu mun san yaudarar kanmu muke. Muna bukatar daukar mataki ne nan take ba wani jira ba. Matakan soji dana tattalin arziki gami da na agajin gaggawa. Rena mu da Isra'ila ta yi shi ne zai sanya ta yi shekara guda tana wa yan uwanmu kisan kare dangai don ta san ba abun da za mu tsinana, duk da cewa yawan musulmun duniya mun zarta biliyan daya da rabi.”

Shi ma shugaban Turkiya,Raceip Erdogan,wanda ya yi barazanar tura rundunar sojin kasarsa zuwa Gaza don kawo karshen yaki kamar yadda yayi nasarar yi a Libiya, ya kara da cewa abun kunya ne ace musulmin duniya sun kasa yi wa yan uwansu na Gaza da Lebanon irin abun da kasashen Turai ke yi wa Isra'ila:

Karin Bayani:Kungiyar OIC ta zargi Isra'ila da laifukan yaƙi

Hoto: ANKA

"Isra'ila na ci gaba da mamaye Falalsdinawa da kisan kare dangi a Gaza da Lebanon ne albarkacin tallafin da ta ke samu daga kasashen Yamma, Me zai hana mu ma akalla, idan har bamu shiga mun taya su yaki ba, mu tabbatar da mun basu makaman da za su kare kansu da shigar musu da dukkanin agajin da suke bukata, ba tare da mun shirya taron da za mu waste ba tare da mun kulla komai ba. Domin yin hakan shi ne yan uwan taka na hakika, ba zancen fatar baka da bai tsinana komai ba”

Shima shugaban Nigeria Bola Ahmed Tinubu wanda ya halarci taron ya ce lokacin maganar fatar baki ya wuce, muddin ana son kawo karshen kisan kare dangi ga wadanda basu san hawa ko sauka da ake ci gaba da yi a yankin Gabas ta Tsakiya ba:

Hoto: Greg Baker/AP Photo/picture alliance

"Yin Allah wadai ba zai wadatar ba wajen kawo karshen kisan kiyashi da akewa bayin Allah a Gaza da akwai bukatar mu yi aiki da cikawa don kawo karshen wannan abun takaicin. Hakan kuma ana bukatar yin hakan da gaggawa.”

Sai dai a hannu guda, shugaban taron, Yarima mai jiran gado na kasar Saudiya Mohammed bin Salman ya nuna cewa, alhakin kawo karshen zaaluncin da Isra'ila ke yi wa kasashen Larabawa dana muuslmi, ya rataya ne ga kasashen duniya wadanda ya wajaba su gaggauta daukar matakan aiki da cikawa.

Watakila hakan ne ya sanya Shehul Azzhar, Sheikh Ahmad Dayyeb, na babbar cibiyar binciken addinin musulunci ta duniya ya mayar masa da martani kan cewa:
”Duniyarmu a wannan zamanin ta rasa jagoranci managarci. Zukatun jagororinta sun kekashe duk da ikirarinsu na wayewa da ci gaba. Su ke kara kera makamai da tura su a dinga kashe yara kanana da mata ko a jikinsu. Bana tsammani za mu iya dogara ga irin wadannan jagororin wajen ceton rayukan wadanda ke fuskantar kisan kare dangi da kone gawarwakinsu.”

Hoto: Johanna Geron/REUTERS

Karin Bayani:Yariman Saudi Arebiya ya bukaci gaggauta kawo karshen yakin Gaza da na Lebanon

Muna kira ga kasashen duniya da su gaggauta daukar matakan kawo karshen yakin Gaza da kuma na Lebanon.