1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron Kungiyar AU

March 10, 2006

Shugaban hukumar kungiyar taraiyar Afrika ya baiyana rashin jin dadinda dangane da halin da yan gudun hijira na Darfur suke ciki.

Alpha Umar Konare ya fadi haka ne a lokacin ziyararsa zuwa birnin Berlin.

A yau ne dai ake sa ran kungiyar Taraiyar Afrika AU zata yi taronta a birnin addis Ababa na kasar Tanzania domin yanke shawara akan ko ta bukaci Majalisar Dinkin Duniya karbar ragamar aiyukan wanzar da zaman lafiya a Darfur.

Amurka da Kungiyar Taraiyar Turai dai suna ci gaba da matsawa kasar Sudan lamba data amince da kasancewar dakarun Majalisar Dinkin Duniya a Darfur,inda yan tawaye da kungiyoyi masu dauke da makamai suke ci gaba da kashe kashen rayuka a yankin.