Taron London kan makomar Somaliya
February 22, 2012Mahalarta taron sun haɗa da sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya Ban Ki-Moon da kuma sakatariyar harkokin wajen Amirka Hllary Clinton. Ƙasar Birtaniya wadda ke ɗaukar baƙuncin taron ta baiyana halin tsaro a Somaliya da cewa muhimmin al'amari ne a gare ta. Lokaci dai na daɗa ƙaratowa. A cikin watan Augusta mai zuwa ne wa'adin gwamnatin wucin gadin ƙasar Somaliyan ke ƙarewa kuma babu wanda zai yi inkarin cewa al'amura basu taɓarɓare ba a ƙasar, kama daga matsalar yunwa zuwa gwagwarmayar 'yan Islama da kuma barazanar wanzuwar wagegen giɓin shugabanci. A kwanannan ne ma wasu masu sa ido na majalisar dokokin Somaliyan suka nunar da cewa akwai sauran tafiya mai nisa a hanyar mayar da ƙasar wadda ke da muhimmanci a yankin ƙahon Afirka kan tsarin tafarki na dimokraɗiyya irin na yammacin Turai. Hatta ma gyaran kundin tsarin mulki wanda lauyoyi masana shari'a na nan Jamus ke taimakawa ƙasar yana buƙatar ƙarin ƙaimi.
Ƙasar Birtaniya wadda ita ce mai masaukin baƙi na wannan taro na da nata buri ko manufa. Wannan kuwa shine damuwar da ta ke da ita, yadda ake samun ƙaruwar yara matasa 'yan Somaliya waɗanda ke da Fasfunan Birtaniya suke tafiya ƙasar ta ƙahon Afirka domin samun horon ta'addanci. Waɗanan matasa sun kasance masu matuƙar barazana da haɗari ga tsaron ƙasa. Birtaniya ta damu game da sha'anin tsaron ƙasarta musamman dangane da gabatowar gasar wasannin Olympics na lokacin bazara wanda za'a gudanar a ƙasar a cikin wannan shekarar.
Musamman ga dukkan alamu za'a maida hankali a muhawarori a game da dangantaka tsakanin ƙungiyar Islama ta Alshabaab da kuma rassan ƙungiyar al-ƙa'ida. A wannan taron za'a yi ƙoƙarin rarrabewa tsakanin 'yan fafutukar Somaliya a nahiyar Turai da takwarorinsu na ƙasashen larabawa inda ƙasashen Qatar da Turkiya za su shiga tsakani domin rage tasirin Amirka da ƙasar Ethiopia waɗanda suka ƙi amincewa a tattauna da 'yan Al-Shabaab. Emmanuel Kisangani wani manazarci ne ɗan ƙasar Somaliya a cibiyar nazarin al'amuran tsaro dake birnin Nairobi. " Amirka da wasu ƙasashe kamar Birtaniya basa son a tattauna da Al-Shabaab saboda suna ɗaukarta a matsayin ƙungiyar 'yan ta'adda. Suna ganin tattaunawa da ita tamkar an yarda da halascin ta ne. Yayin da waɗanda ke buƙatar a tattauna suke da hujja ƙwaƙwara, saboda Al-Shabaab su suke iko da mafi yawancin ƙasar Somaliya. Akwai wurare inda suka samar da tsaro da rage aikata ta'asa da sauransu wanda jama'a suka yaba. A saboda haka ka ce za ka yi amfani da matakin ƙarfin soji ga rikicin Somaliya za'a wuce gona da iri".
A waje guda maƙwabtan Somaliya tuni suka baiyana ɗaukar matakin kutse inda suka tura sojojin daga kudanci domin afkawa mayaƙan Al-Shabaab. Ita ma ƙasar Ethiopia wadda ke ɗaukar kanta a matsayin mai ƙarfin iko a yankin tare da sahalewar Amirka da kuma ƙungiyar IGAD a shekarar 2006 ta tura sojoji zuwa kan iyaka domin tunkarar mayaƙan jihadin.
Ita ma dai tawagar jamus za ta gabatar da ta ta da'awar ce akan muradun tsaro. Jamusawan za tafi da sabon jadawali na tunkarar matsalar ta Somaliya a taron na London. Jamus dai na goyon bayan shirin majalisar tsaro da zaman lafiya na ƙungiyar gamaiyar Afirka. Wakilin ma'aikatar harkokin wajen Jamus akan al'amuran Afirka Walter Linder ya yi bayani yana mai cewa " Wannan taro a haƙiƙa shine na ƙarshe a jerin matakai zuwa lokacin bazara, amma kuma lamari ne wanda bayan shekaru 22 da ƙasar Somaliya ta yi tana cikin wannan hali ya zama wajibi a gudanar da shi domin nazarin makoma yadda ƙasar za ta cigaba. Batun halin da jama'a ke ciki da fashin 'yan jiragen ruwa a kan teku da ayyukan tarzoma da batun 'yan gudun hijira dukkan waɗannan al'amura ne da za mu duba waɗanda sun damu kowanne mu a saboda haka na ke fata wanna taro zai ba da cikakkiyar gudunmawa".
Sai dai kuma a waje guda wasu manazarta da dama 'yan ƙasar Somaliya sun yi kakkausar suka ga taron domin a cewar su bayan shekaru kusan 23 babu wani jadawali ingantacce da aka samar a ƙarshen wa'adin gwamnatin riƙon ƙwarya da zai ƙare a watan Augusta. A nan ma dai Emmanuel Kisangani na cibiyar nazarin a'amuran tsaro dake Nairobi ya yi bayani yana mai cewa " Ina da shakku domin babu wanda ke da yakinin abin da zai faru bayan ƙarewar wa'adin a watan Augusta. Abin da duk mutane suke buƙata shine wa'adin gwamnatin riƙon ƙwarya zai ƙare a cikin watan Augusta, to amma babu wani abu a hannu da za su nuna wanda zai baka hasken abin da zai zo bayan ƙarewar wa'adin".
Mawallafa: Ludger Schadomsky/Abdullahi Tanko Bala
Edita: Yahouza Sadissou Madobi