Taron magance sace kudi a Afirka
November 18, 2026
Wani kawance ne tsakanin kasashen nahiyar Afrika suka kula na kokari na kwato dimbin dukiyar da ake sacewa daga nahiyar ana jibge su a kasashen waje. Karbi dukiyoyin na zama babban kalubale duk da shaidu cewa sace su aka yi aka jibge a kasashen.
Najeriya na jagoratar wannan aiki ne tare da ba da cikakken goyon bayanta da ya sanya tattara wakilan kasashen Afirka a Abuja. Dr Adamu Aliyu shi ne shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Najeriya wanda ya nuna muhimmancin dakile matsalolin.
Manyan matakai
Wakilan kasashen Afirka sun zo da dubaru iri daban-daban a kokari na hada karfi don tunkarar matsalar kama daga kanana da manyan da ke cikinsu. Francis Ben Kaifala shi ne shugaban hukumar yakı da cin hanci ta kaşar Saliyo, wanda yake cewa wannan zama ya tattara kan abin da za a iya yi.
Abin da ya ba da kwarin gwiwa shi ne samun shigar kasashen yankin Sahel da a baya-bayan nan suka ware kansu. Wannan na nufin dinke duk wata baraka.
Duk da wannan ci-gaba ga Auwal Musa Rafsanjani da ke jagorantar kungiyoyin farar hula ya bayyana man damuwarsu a kan sace kudin da ake kwatowa da ya ce akwai bukutar sake lale.
Hada kai dai shi ne taken kungiyar kasashen Afirka da suke bayyana muhimmanci a gudu tare a tsira tare.