1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron Majalisar Dinkin Duniya akan Siriya

October 4, 2011

Ƙwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya gabatar da wani saban kuduri na hukunta magabatan Siriya game da tashin hankali da ake fama da shi a kasar.

Masu gudanar da zanga zangar ƙin jinin gwamnati Bachar Al'Assad a SiriyaHoto: picture alliance/abaca

ƙasashen yammancin duniya na ƙokarin ƙara matsa ƙaimi doimin amince wa da ƙudrin da zai yi allah wadai da tursasa war da gwamnatin Siriya ta ke yi ga masu zanga zanga ƙin jinin gwamnatin Bashar Al Assad.

Taron na kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniya wanda ƙasashen Faransa da Jamus da Ingila da Portugal ke son a ɗauki tsatsaura matakai akan Siriya,na iya gamuwa da cikas na ƙasar Rasha wacce ta yi barazanar yi amfanin da masayin ta na faɗa a ji a kwamitin wajan hawan kujera na ƙi.ƙudirin wanda ƙasashen turai suke son kwamitin na sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya amince da shi.

ya tanadi ɗaukar matakai akan ƙasar Siriya na da ƙwanaki 30 inda bata dakatar da aikata kisa ba akan jama'ar ƙasar Yanzu haka dai a kwai rohotannin da ke nuna cewa yan adawar na kasar ta siriya sun fara tinkarar sojojin gwamnatin da makamai wanda suka fara yin amfani da su domin kiffar da mulkin.Kawo yanzu dai MDD ta ce mutane 2700 suka mutu a cikin yamutsin na masu neman sauyi a ƙasar ta Siriya.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Yahouza Sadissou Madobi