1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron majalisar ministocin EU kan kuɗin Euro da Gabas Ta Tsakiya

September 12, 2011

Matsalar mummunan halin da kuɗin Euro yake ciki, al'amari ne da majalisar ministocin ƙungiyar tarayyar Turai basa iya kauce mata a duk inda suka shirya taro domin tattauna wasu al'amuran dabam a tsakanin su.

Tutar kungiyar EU da ta Girka: alamar hadin kai a kokarin shawo kan matsalar kudin GirkaHoto: dapd

Ministocin harkokin waje ko wakilansu daga ƙasashen ƙungiyar haɗin kan Turai ranar Litinin a Brussels suka tattauna tsakanin su. Babban abin da aka maida hankali kansa a ganawar ministocin, shine halin da ake ciki game da faɗi-tashin kudin haɗin gwiwa na Euro da kuma matsalolin ƙasar Girka.

A ƙarshen mako, an riƙa samun shakku, musamman daga nan Jamus, a game da ko ƙasar Girka za ta iya cika sharuɗɗan da aka shimfiɗa mata na tsimin kuɗi, domin shawo kan matsalar ɗimbin bashi da take fama da shi. Har ma ministan tattalin arziki, Philipp Rösler ya gabatar da shawarar maida ƙasar ta Girka wadda bata da sauran kuɗin tafiyar da aiyukan ta na yau da kullum. To sai dai a lokacin taron majalisar ministocin a Bruessels, karamin minista, Werner Hoyer ya ce Jamus ba zata bi wannan mataki ba.

Yace inda a tsawon shekarun nan ace a kungiyar hadin kan Turai muna da wani tsari na baiwa wata ƙasa dake cikin haɗin kan kuɗi na Euro damar maida kanta wadda bata iya tafiyar da al'amuran ta na yau da kullum saboda rashin kuɗi, to da kuwa mun ci gaba matuka daga inda muke a yanzu. Tun da kuwa bamu dashi, bai kamata a tsaya ana ta maida hankali kan wannan al'amari ba, saboda hakan yana iya kawo hadarin da zai shafi wasu kasashen ma dabam. Saboda haka ne yake da muhimanci a riƙa taka tsan-tsan wajen zaɓen kalmomin da ake amfani da su.

Shi kuwa shugaban jam'iyar CSU, Horst Seehofer wani tsarin ne dabam ya gabatar da shawarar sa, wato a tsame kasar ta Girka daga hadin kan na kudin Euro. To sai dai ga ministan harkokin wajen Austria, Michael Spindelegger, wannan shawarar ita ma ba abin a duba ta bane.

Shugaban babban bankin Turai, Jean-Claude TrichetHoto: dapd

Idan har mutum zai kawo irin wnanan shawara, to kuwa tilas ne yayi tunanin cewar a yarjejeniyar taraiyar ta kudin Euro, babu inda aka tanadi koran wata kasa. Hakan yana nufin wajibi kenan a sami yadda za'a shawo kan matsalar ta hanyar shawarwari da Girka, kuma kamar yadda aka ga alamu yanzu, Girka din bata ma da niyyar fita daga taraiyar ta kuɗin Euro.

Spindelegger da Hoyer suka ce zasu jira sakamakon ganawar da za'a yi tsakanin ƙasashen ƙungiyar haɗin kan Turai uku da babban bankin Turai da hukumar kudi ta duniya tukuna. Mashawartan bangarorin ukku a farkon wannan wata cikin fushi suka daina tattaunawar su saboda bacin ran rashin samun wani ci gaba daga gwamnatia birnin Athens. To amma daga baya suka dawo, kamar yadda shugaban majalisar kungiyar hadin kan Turai Herman van Rumpoy.

A game da harkokin ware, ministocin yanzu dai sun fi baiyana damuwar su ne a game da rashin jituwar dake tsakanin Israila da da Masar da Turkiya. Ministan harkokin wajen Austria Spindelegger musamman yana ganin mamaye ofishin jakadancin Israila a birnin Alkahira da yan zanga-zanga suka yi a matsayin wata alama mai muni.

A yadda nake gani, babban abin damuwa ne idan har a wata kasa mahukunta suka kasa kare ofisoshin jakadancin kasashen ketare. Yin haka shine tushen farko na kafa huldar jakadanci tsakanin kasa da kasa. Abu mafi dacewa shine kasashen su mutunta wakilcin jakadancin juna, su zauna kan teburin shawarwari, amma ba su nemi warware matsalolin su ta amfani da karfi a kan tituna ba.

Abin da ya faru a birnin na Alkahira, ana sa ran zai shafi dangantaka tsakanin kungiyar hadin kan Turai da sabbin shugabannin Masar. Kungiyar hadin kan Turai zata yi tambayar ko Masar, a bayan kawar da mulkin Hosni Mubarak tana kan hanyar democradiya da kiyaye shari'a a zahiri .

Pirayim Ministan Turkiya, Recep Tayyip ErdoganHoto: AP

Wannan yanki ya kuma kasance cikin mawuyacin hali, saboda sabani tsakanin Israila da Turkiya. Turkiya a farkon wannan wata ta kori jakadan Israila daga birnin Ankara, abin da ya zama kololuwar rikici tsakanin su, bayan da sojojin Israila suka yi amfani da karfi suka mamaye wani jirgin ruwa dauke da kayan agaji zuwa yankin Gaza, inda yan asalin Turkiya da dama suka mutu. Dangane da haka ne karamin minista Werner Hoyer na Jamus yayi kira ga kasashen biyu su nunawa junan su hali na sanin ya kamata.

Ministan harkokin wajen Jamus, Guido Westerwelle yanzu haka yana gabas ta tsakiya, inda shima kamar dai kakakin ƙungiyar haɗin kan Turai a harkokin waje, Catherine Ashton zai tattauna da shugabanni a birnin Alƙahira.

Mawallafi: Christoph Hasselbach/Umaru Aliyu
Edita: Mohammad Nasiru Awal

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani