1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Tattalin arziki

Taron manyan kasashe masu karfin arziki a Jamus

Abdourahamane Hassane
March 17, 2017

Kasashe masu karfin masana'antu na ganawar bullo da dabarun bai wa kasashen Afirka rance don farfadowa daga tawayar da suke ciki a yanzu.

Zaman taron G20 a Jamus
Zaman taron G20 a JamusHoto: DW/A. Freund

Ministocin kudi na kasashen kungiyar G20 masu arzikin masana'antu da Shugabannin bankuna zasu soma wani taro a wannan Juma'a 17 zuwa Asabar 18 ga watan Maris a Baden-Baden na Jihar Baden Wutemberg dake a nan Jamus domin tattauna batun bayar da rance ga kasashe masu tasowa don tayar da komadar tattalin arzikinsu. Sai dai wata kungiya mai zaman kanta dake a nan Jamus Erlassjahr ta ce kasahen masu tasowa  kusan guda 40 basuka sun yi masu yawa fiye kima.

Halin da ake ciki dai a yanzu na tattalin arzikin duniya na kama ne da wanda ya faru a wajajen karshen shekarun 1970 zuwa 1980, lokacin da aka fuskanci matsalar basuka da raunin tattalin arziki a kasashen duniya, musamman a kasashe masu tasowa.

Manazarta na cewa basukan ba su taimakawa bunkasar tattalin arzikin kasashen masu tasowa saboda yawan kudaden ruwa da suke biya kamar yadda Jürgen Kaiser Shugaban wata kungiyar Erlassjahr da ke bin diddigin yadda ake bada basukan ga kasahen duniya ya bayyana.

      Ya ce ''Kudaden ruwan mafi kankanta kasashe masu arzikin masana'antu su kan biya, yayin da a tsarin da aka yi a Afirka kasahen kan biya kashi bakwai zuwa 15 na kudaden ruwan, abin da ya sha bamban tsakanin kasashen arewa da kudu''

Faduwar farashin man fetir da na iskar Gas da Kwal da sauran abubuwa na arzikin karkashin kasa a nahiyar Afirka na zaman wani tarko na cin bashin kananan kasashen daga manyan hukumomin kudade na duniya. Misali kasar Mozambik duk da irin basussukan da take ciki, har yanzu tana cikin wani hali, baya ga kasancewarta a sahun kasahe 40 na Afirka wadanda suka fi kowa yawan bashi a duniya ba tare da wani ci gaba natattalin arziki ba.  Joao Mosca wani masanin tattain arziki daga kasar Portugal, ya ce rashin biyan basuka na kasar Mosambik na iya janyo mata bakin jini.

 Ya ce ''dole Mozambik ta biya bashin da ke kan ta  saboda kuwa alkawari ne ta dauka kuma harka ce ta jari-hujja. Akwai abin da zai iya biyo baya muddin ta ki biyan kudaden. Ba ma ita kadai ba, duk wadanda suka ki biyan kudaden kudaden da ake bin su, za su gamu da kalubale''

Tun daga shekara ta 2005 zuwa 2015  kasashen Angola da Kenya da Afirka ta kudu sun ninka basukan da suke ci daga bankin duniya har sau uku. Misalii karamar kasa kamar Cape Verd, ta ciwo bashin da ya wuce na shekarun baya-bayan nan.

Masu sharhi kan al'amura na hasashen cewar taron na kwanaki biyu na Baden Baden, zai tattaunawa duk irin matsalolin da kasahen masu tasowa ke fuskanta domin tunkarar wani sabon zango na bayar da bashin ga wasu daga cikin kasahen masu tasowa.

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani