1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
TarihiJamus

Berlin: Taron matasan Afirka kan raba nahiyar

February 12, 2025

Shekaru 140 da gudanar da wani taro kan Afirka mai taken "Taron Afirka a Berlin", inda kasashen Turai da Amurka da Daular Usmaniyya ta wancan lokaci suka amince da gindaya ka'idojin raba nahiyar Afirka a tsakaninsu.

Taro | Jamus | Berlin | Rabon Afirka | 1884
'Yan Afirka na tuna yadda aka raba gadon nahiyarsu a taron Berlin na shekara ta 1884Hoto: Royal Palace/Musei Reali Torino

Gidauniyar Afirka ta Jamus da jami'ar Dar es Salaam tare da hadin gwiwar Farafina Afrika-Haus, sun shirya wata mahawara a Berlin fadar gwamnatin Jamus domin tuna yadda aka shata iyakokin Afirka, inda daga bisani aka shirya wa matasan da suka halarta rangadin birnin musamman tarihinsa na mulkin mallaka. Mugarura Charles wanda ya fito daga Yuganda na cikin tawagar, domin sanin asalin tarihin mulkin mallakar Jamus.

Karin Bayani: Lamuran da suka biyo bayan mulkin mallaka

A wani titi da ke tsakiyar Berlin din an rufe wani allon hoton zaman tsara rabon Afirka, wanda aka yi shekaru 140 da suka wuce. A cikin fadar shugaban gwamnati ba tare da wani dan Afirka da ya a teburin ba, wakilan Turai da Amurka da kuma Daular Usmaniyya a lokacin sun yi zama na yanke shawarar mulkin mallaka na gaba. Iyakoki masu sabani da rigingimu da cin zarafi, sune ke bibiyar rayuwar da ake fuskanta ya zuwa yau. 'Yan Afirka mazauna kasashen waje na ci gaba da tuna wannan yanayi, ta hanyar adana dukkanin allunan tarihi.

Yadda aka gididdiba nahiyar Afirka a taron Berlin a shekara ta 1884Hoto: akg-images/picture-alliance

Albarkacinsu, a wannan rangadin matasan sun ganewa idanunsu. Haka labarin yake ga mai fafutukar neman daidaito: Martin Quane a Dibobe, direban jirgin kasa na farko dan Afirka a Berlin. A cikin takardar kokensa a shekarar 1919, ya nemi 'yancin kai da daidaito ga mutane a ciki da kuma daga yankunan da Jamus ta yi wa mulkin mallaka. 'Yan Afirka mazauna Turai irin su Nikitta Dede dan asalin kasar Ghana, sun bukaci masu mulkin mallakar da su sauya taku musamman a dangantakarsu da kasashen.

Karin Bayani: Neman mafita a tasirin mulkin mallakar Jamus

Tasha ta uku kuma ta karshe na masu rangadin birni suka ziyarta, na da suna wanda jagorar yawon bude ido dan kasar Namibiya da masanin tarihi Zeller suka yi wa kallon wariyar launin fata. Sunan layin "M-Street", bayan a zahiri ba sunan titin ba ne. Sai dai kuma, ana ci gaba da muhawara kan sauya sunan. Mamba ta kwamitin tuntuba na matasa a Tarayyar Afirka Karen-Andréa Bedoume ta ce, tana son ganin karin hobbasa a irin wannan sauyi tare da fatan za a cimma yin sulhu da kuma iya cimma daidaito shekaru 140 bayan taron na birnin Berlin.