1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sauyin yanyi na faruwa cikin gaggawa

Abdullahi Tanko Bala
September 26, 2019

Fiye da shekaru 30 da suka wuce binciken masana  kimiyya suka fayyace karara tasirin da sauyin yanayin ke yi. Illolin sauyin yanayin dai sun dade suna barazanar shafe rayuwar hallitu a doron kasa

New York Klimagipfel
Hoto: Reuters/L. Jackson

Greta Thunberg yar kasar Sweden mai fafutukar kare sauyin yanayin ta yi jawabi a gaban shugabanni yayin bude babban taron Majalisar Dinkin Duniya kan sauyin yanayi a birnin New York na Amirka inda ta caccaki shugabanni da gazawa wajen daukar matakan kare sauyin yanayi.

Fiye da shekaru 30 da suka wuce binciken masana  kimiyya suka fayyace karara tasirin da sauyin yanayin ke yi. Illolin sauyin yanayi sun dade suna barazanar shafe rayuwar hallitu a doron kasa

Daruruwan matasa sun gudanar da zanga zangar lumana a sassan kasashen duniya domin jawo hankali kan sauyin yanayi da aka yiwa lakabi da Friday for future, inda suka bayyana damuwa a kan halin da yanayi ke ciki tare da bukatar gwamnatoci su dauki matakai domin shawo kann lamarin.