Taron ministoci a Berlin a kan Ukraine
January 9, 2015Talla
Ministocin harkokin wajen Faransa da Jamus da Rasha da Ukraine za su gana a birnin Berlin fadar gwamnatin kasar Jamus a ranar Litinin inda za su tattauna kan rikicin gabashin Ukraine, da aiwatar da shirin yarjejeniyar birnin Minsk.
A wata tattaunawar zauren hadaka ta wayar tarho ministocin sun amince su gana a kokarin da ake na ganin an kama bakin warware rikicin gabashin kasar ta Ukraine kamar yadda ministan harkokin wajen Jamus Frank-Walter Steinmeier ya bayyana.
Minista Steinmeier Ya ce a wannan rana za su sake zama don ganin an warware matsalolin da suka dabaibaye rikicin kasar ta Ukraine. Sai dai akwai gargada da za a iya fiskanta a hanyar da ake bi wajen ganin an aiwatar da cikakkiyar yarjejeniyar da aka kulla ta birnin na Minsk.