1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron ministocin ECOWAS kan sadarwa

Abdoulaye Mamane Amadou June 23, 2016

Taron da ke gudana a birnin Niamey zai kuma duba halin tsadar sadarwa da rashin kyawun layi da ake samu a tsakanin kasashen da ke yankin domin samar da mafita.

Internetnutzung in Afrika
Hoto: AFP/Getty Images

A Jamhuriyar Nijar ministocin sadarwa na kasashe 15 manbobin CEDEAO sun soma wani zaman taro na koli na kwanaki biyu don duba batun matsalolin sadarwa da batun farfado da gidajen waya da ke fuskantar kalubale a kasashen na yammacin Afrika.Taron na ministocin kasashen na CEDEAO ko ECOWAS na zuwa ne a yayin da matsalar sadarwa ke kara kamari inda tsadar farashin sadarwa daga wata kasar zuwa wata ke ciwa al'ummomin yankin tuwo a kwarya a yayin da a share daya wasu miyagu ke amfani da wasu fasahohin sadarwa don cimma miyagun manufofi kamar yaudara da aikata aiyyukan ta'addanci.

Uwa uba matsalar durkushewar gidajen waya da ke addabar yankin na nahiyar Afirka ta yamma inda kadari da aiyyukan gidajen waya a yanzu suka ruguje, wadannan matsalolin da ma wasu dadama ne ministocin ke shirin dukufa akan su don samo masalaha.


Yahouza Sadissou Madobi shi ne minitsan ma'aikatar sadarwa da gidan wayar Jamhuriyar Nijar wanda ya ce: "Akwai tsada na wayar tarho to wadanne hanyoyi za mu bi don rage tsadar don a kara samun sauki a kudaden sadarwa a tsakanin kasashenmu Sannan da shi kanshi ingancn wayar ta yanda za'aji wayar tangararau. ''Batun durkushewar gidajen waya da ada jama'a ke amfani da su don aike da sakonni sakamakon canzwar al'amurra a yanzu na daga cikin wata babbar matsalar dake addabar kasshen na Afirka ta yamma.Ministan harkokin sadarwa da gidan waya na kasar Cote d'ivoire ke nan kuma shugaban majalisar ministocin sadarwa na kasashen CEDEAO Brinaut Dabagnokoney ke cewar abin da muke jira ga taron na birnin Niamey shi ne na ganin an kaddamar da cikakken nazari kan duk wata damar da fasahohin zamani za su ba mu don ci-gaba da kyautata kimar gidajen wayarmu.

Daga cikin wadannan fasashohin kuwa inji Ministan da akwai tsarin sabbin fasashohin zamani da sune suka yi musabbabin durkushewar gidajen waya kana kuma su ne kadai za'a iya yin amfani don sake farfado da tsarin ta hanyar zamani.