1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron ministocin harkokin wajen NATO a Berlin dangane da Libiya

April 14, 2011

Ministocin harkokin wajen ƙasashen dake cikin ƙungiyar ƙawancen tsaron NATO sun gudanar da taro a birnin Berlin na Jamus inda suka cimma matsayar ƙara yin matsin lamba ga shugaba Gaddhafi na Libiya ya sauka daga mulki

Zauren taron ministocin harkokin wajen NATO a BerlinHoto: AP

Taron dai ya amince da bin tafarkin diflomasiyya a matsayin hanyar warware rikicin. Babban sakataren ƙungiyar ƙawancen tsaron NATO Anders Fogh Rasmussen, wanda ya gana da ministocin kula da harkokin wajen ƙasashen ƙungiyar a birnin na Berlin, ya yi alƙawarin cewar NATO za ta ci gaba da ƙaddamar da hare hare a Libiya har sai ta tilastawa sugaba Gaddhafi barin kujerar mulkin ƙasar, tare da daina kaiwa fararen hula hare hare, kana da tabbatar da cewar dakarun gwamnatin Libiya sun janye daga fagen yaƙi zuwa barikokin su, gami da bayar da damar kaiwa jama'a agajin da suke buƙata.

Babban sakataren ƙungiyar NATO Anders Fogh rasmussen a zauren taron BerlinHoto: dapd

Waɗannan abubuwa dai na daga cikin sanarwar bayan taron da ƙungiyar ta amince da su, bayan ganawar ministocin harkokin wajen ƙasashen NATO da kuma wasu ƙasashe shidan dake tallafawa ƙungiyar wajen hare haren da take ƙaddamarwa a ƙasar ta Libiya. Sai dai kuma a cewar Anders Fogh Rasmussen akwai abinda suke buƙata domin cimma wannan burin kasancewar dakarun Gaddhafi sun ɓullo da salon ɓoye makaman su a yankunan da fararen hula suka fi yawa:

Domin kaucewa kissar fararen hula muna buƙatar ingantattun kayayyakin yaƙi - irin na zamani. Muna buƙatar jirgin yaƙi da zai bamu damar ƙaddamar da hari daga ƙasa domin biyan buƙatar kai hari daga sama har zuwa ƙasa ."

A cewar Rasmussen, babban kwamandan dakarun ƙungiyar NATO Admiral Jsames Stavridis ne ɗan ƙasar Amirka ne ya gabata da bukatar domin kaucewa kissar fararen hula, kana da ƙarfafa farmakin da ƙungiyar ke kaiwa akan muhimman wuraren dake ƙarƙashin ikon shugaba Gaddhafi, inda ya ce ko a jiya ma ƙungiyar ta yi namijin ƙoƙari ta wannan fuskar:

"Hatta a jiya ma mun ci gaba da kai hare haren jiragen sama akan masu ƙaddamar da hare hare da makaman roka da kuma akan na'urorin kula da zirga-zirgar jiragen sama a wasu muhimman wuraren da suka da kusa da birnin Misrata da kuma Tripoli."

Za a ci gaba da kai wa dakarun Ghaddafi hari


Sai dai duk da cimma matsayar ci gaba da kaiwa dakarun Gaddhafi harin da taron ƙungiyar NATO ta yi, ta jaddada buƙatar yi amfani da hanyar diflomasiyya domin shawo kan rikicin ƙasar ta Libiya. Saɓanin matsayin da ƙasashen Faransa da Birtaniya suka ɗauka na ƙara yin amfani da ƙarfin tuwo, Jamus - mai masauƙin baƙin, ta jaddada na ta matsayin ta bakin ministan harkokin wajen ta Guido Westerwelle:

"Alal-haƙika matsala ɗaya ce ta banbanta maganar Libiya. Matsalar kuwa ita ce waɗanne hanyoyi ne zasu kai ga cimma wata matsaya ɗaya. Wannan shi ne ainihin inda take ƙasa tana dabo. Jamus dai ta yanke shawarar cewa ba zata tura sojojinta a cikin faɗan ba. Amma hakan ba ya nufin cewar mun ɗauki wani matsayi na ba ruwanmu. Daidai da Faransa da sauran ƙasashen MƊD mu ma muna tattare da ra'ayin cewar sai fa idan wannan ɗan kama-karyar ya fice ne Libiya zata samu kyakkyawar makoma."

Baya ga rikicin ƙasar Libiya, taron ƙungiyar NATO ya mayar da hankalin sa ne ga matsalar ƙasar Afghanistan, wanda ministocin harkokin wajen ƙasashen ƙungiyar za su ci gaba da tattaunawa har ya zuwa Jumma'ar nan, domin nazarin matakan da suke ɗauka da nufin mayar da alhakin kula da sha'anin tsaro ga dakarun gwamnatin Afghanistan - kamar yanda taron na birnin Lisbon ya amince a shekarar da ta gabata.

Mawallafi: Saleh Umar saleh

Edita: Ahmad Tijani Lawal