1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Sahel: Taron ministocin kudi na AES

Salissou Boukari LMJ
November 27, 2023

Ministocin tattalin arziki da kudi na kasashen Burkina Faso da Mali da Jamhuriyar Nijar, sun gudanar da wani babban taro nasu na mambobin kungiyar hadin kan kasashen Sahel ta AES.

 Kwance | Assimi Goïta | Mali | Abdourahamane Tiani | Nijar | Ibrahim Traoré | Burkina Faso
Assimi Goïta na Mali da Abdourahamane Tiani na Nijar da Ibrahim Traoré na Burkina FasoHoto: Francis Kokoroko/REUTERS; ORTN - Télé Sahel/AFP/Getty; Mikhail Metzel/TASS/picture alliance

Taron ministocin kudin na kasashen Burkina Faso da Mali da Jamhuriyar Nijar da ke zaman na farko ya mayar da hankali kan batun ci-gaban tattalin arziki a yankin Liptako-Gourma da ya hada kasashen uku. Ministocin kasashen uku dai sun yaba da yadda taron ya kasance, wanda suka ce ya gudana yadda ya kamata duk kuwa da mawuyacin halin tattalin arziki da tsaro da kasashen uku ke fuskanta. Hakan na nuni da irin tsayin dakan da wadannan kasashe uku na Burkina Faso da Mali da Jamhuriyar ta Nijar suka yi, inda suka jaddada kakkausar suka kan hare-haren ta'addancin da ake kai wa a yankin na Liptako-Gourma tare da nuna goyon bayansu da kuma aniyarsu ta yin aiki tare domin jin dadi da walwalar al'ummar yankin.

Masu goyon bayan sojojin da suka kifar da gwamnati a Nijar da tutocin kasashen ukuHoto: AFP/Getty Images

Boubacar Saidou MOUMOUNI karamin minista da ke karkashin firaminista kuma ministan kudi na Jamhuriyar Nijar ya nunar da cewa daga cikin burin da suke da shi akwai samar da tsari na doka kan samar da kudin tafiyar da kungiyar da inganta zirga-zirgar al'umma ba tare da cikas ba a tsakanin kasashen na AES. A nasu bangaren masana tattalin arziki kamar Issoufou Boubakar Kado Magaji sun yi amannar cewa, samar da kudi na bai daya na zamann mafita ga kasashen. Tuni dai 'yan kasuwa suka soma tunanin ganin sauyin da za a samu a nan gaba zai ba su damar inganta harkokin kasuwancinsu ta hanyar kera kayayaki maimakon komai sai an shigo da shi daga kasashen waje. Sai dai a hannu guda wasu na ganin cewa wannan hanya ta yunkurin ficewa da kasashen uku ke yi domin kafa tasu kungiyar, na bukatar taka tsan-tsan domin gudun da na sani.