Taron ministocin kunɗin EU a Brussels
May 9, 2010Talla
A yanzu haka ministocin kuɗi na ƙasashe membobin Ƙungiyar Tarayya Turai, na cigaba da zaman taro a birnin Brussels da zumar laluben hanyoyin ceto takardar kuɗin Euro daga barazanar kariyar darajar da take fuskanta a halin yanzu, da kuma ɗaukar matakan riga kafi, na hana yaɗuwar matsalar tattalin arzkin Girka, ga sauran ƙasashen EU.
Wannan taron gaggawa ya biwo bayan haɗuwar shugabanin ƙasashen EU, ranar juma´a da ta wuce a birnin Brussels, inda suka ɗauki alƙawarin aiki tuƙuru, domin kare ƙasahasen daga kariyar tattalin arziki.
Saidai ministan kuɗin Jamus , Wolfgang Schäuble dake halartar taron, ya fukanci motsuwar jiki, inda a yanzu yake kwace a wata asibitin Brussels.
Mawwallafi: Yahouza Sadissou Madobi Edita: Umaru Aliyu