1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron Moscow akan Iran

Zainab A MohammadApril 19, 2006

Rasha/Iran

Rasha tace bazaa gaggauta mata amincewa da daukan matakai na ladabtarwa akan Iran ba,adangane da shirin nuclearnta,bayan kammala taron kasa da kasa a birnin Mosko daya tunzura Amurka,akokarinta na neman goyon baya wajen kakabawa Iran takunkumi.Ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov,yace manyan kasashen duniya guda 5 dake da zaunanniyar kujera a komitin sulhu,da Jamus sun kammala tattaunawarsu a birnin Mosko jiya cikin dare,ba tare da cimma wata madafa ,adangane da batun nuclearn Iran.Akasarin kasashen dai sun bukaci da a jinkirta daukan wani mataki kann Iran,har sai hukumar kula da harkokin Nuclear ta Mdd ta gabatar da rahotan sakamakon Bincikenta.Mr Lavrov ya fadawa taron manema labaru cewa ,dukkan mahalarta taron sun amince dacewa ,Iran na bukatar daukan matakai tsaurara a dangane da martani kann zartarwa hukumar ta IAEA.Amurka dai na tayi imanin cewa Iran na kera makaman atom,duk da hakikancewar Tehran nacewa makamashi take ingantawa.Akan wannan hali da ake ciki shugaba George W Bush na Amurkan yace…..