1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron Munich: Amurka ta bukaci hadin kan Turai

Binta Aliyu Zurmi ZUD
February 14, 2026

Sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio ya gabatar da jawabin hadin kai a tsakanin Amurka da kasashen Turai a taron tsaro na Munich da ke gudana yanzu haka a Jamus.

Deutschland München 2026 | US-Außenminister Marco Rubio bei der Münchner Sicherheitskonferenz
Hoto: Thomas Kienzle/AFP

Babban jami'in diflomasiyyar ta Amurka ya ce kasarsa ba ta da niyyar kawo tangarda a alakarsu da Turai, amma kuma ya ce  shugabannin Turai sun gudanar da wasu manufofi da dama da ke da dimbin kura-kurai da suke bukatar sauyi.

Rubio ya ce Amurka na son Turai ta kasance mai karfi, yayin da yake musanta zargin da ake yi cewa gwamnatin Trump na son raunana kungiyar tsaro ta NATO.

Sakon hadin kai na sakataren harkokin wajen Amurkan ya sami tarba mai kyau a tsakanin kasashen Turai da dama, wanda dangantakar diflomasiyyarsu ke tangal-tangal.

Jawabin nasa ya yi hannun riga da wanda mataimakin shugaban Amurka JD Vance ya gabatar a shekarar da ta 2025. 

Kasashen Turai da dama na neman kyautata alakarsu da Amurka, ko a nashi jawabin shugaban gwamnatin Jamus Friedrich Merz, ya bayyana bukatar samar da sabuwar hadin gwiwar trans-atlantic tsakanin Amurka da Turai. Merz ya bayyana cewar Amurka ba za ta iya tafiya ita kadai a wannan duniyar da muke ciki.

Karin Bayani:Taron tsaro a birnin Munich na Jamus