1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

TARON MUNICH KAN HARKOKIN TSARO NA KASA DA KASA

Yahaya AhmedFebruary 8, 2004
A taron da aka yi a karshen makon da ya gabata a birnin Munich, kan batutuwan da suka shafi harkokin tsaron kasa da kasa, sakataren tsaron Amirka Donal Rumsfeld, ya nanata muhimmancin inganta huldar da ke tsakanin kasarsa da nahiyar Turai. Amma yayin da Amirkan ke kare matakin da ta dauka na yakan Iraqi a gun taron, kasashen Turai, musamman ma dai Jamus, ta bakin ministan harkokin wajenta, Joschka Fischer, har ila yau ba ta yi amanna da yi wa Iraqi wannan daukin ba.

A muhawarar da aka yi kan hanyoyin da za a bi a inganta halin rayuwar jama'a a Gabas Ta Tsakiya, an kuma sami bambancin ra'ayi tsakanin Amirkan da Turai. Shi dai Rumsfeld ya bayyana ra'ayin cewa, hambarad da gwamnatin Saddam Hussein da aka yi ya kawo wata gagarumar fa'ida ga yankin na Gabas Ta Tsakiya baki daya. Ya ce a halin yanzu, akwai wata iskar `yanci da ke kadawa tana yaduwa a duk fadin yankin gaba dayansa. A bangaren Jamus dai, ministan harkokin waje Joschka Fischer ya nuna shakkunsa ga ikirarin da Amirkan ke yi na cewa al'umman yankin tuni sun rungumi tafarkin dimukradiyya. Sabili da haka ne kuwa, ya ba da shawarar kirkiro wasu sabbin hanyoyi don inganta halin rayuwar jama'a a Gabas Ta Tsakiyan, maimakon tura musu dakarun soji kawai.

Manazarta al'amuran yau da kullum na ganin cewa, Fischer dai ya yi amfani da wannan taron ne wajen bayyana wa Amirka matsayin kasashen Turai dangane da yankin Gabas Ta Tsakiya, kafin taron koli na kasashen NATO da za a yi a cikin watan Yuni mai zuwa. Ita ma Amirkan dai, tana tanadin gabatar wa kungiyar NATOn wani shiri na bunkasa ayyukan hadin gwiwa, tsakkanin kungiyar da kasashen da ke yankin bahar Rum. Amma a nan dai tuni Turai ta sha kanta. Hakan ne kuwa, Fischer ke son ya bayyana wa mahukuntan birnin Washington dalla-dalla.

A ganinsa dai, Amirkan ce ya kamata ta ba da hadin kai ga yunkurin da kasashen Turai ke yi na samun sassaucin tsamari a Gabas Ta Tsakiya. Idan ko wannan hadin kan ya samu, za a iya cim ma raguwar hare-haren ta'addanci a ciikin wani dan gajeren lokaci, abin da kuma zai janyo zaman walwala cikin kwanciyar hankali.

Amma ba abin mamaki ba ne ganin irin dari-darin da Rumsfeld ke yi wa wannan shawarar, wato ta mai da hankali kan tuntubar juna da hadin gwiwa, maimakon neman warware duk matsaloli da matakan soji. Babu dai wanda ya yi zaton cewa, sakataren tsaron na Amirka zai yi amanna da wata shawarar da ba ta fito daga kasarsa ko kuma daga abokan burminta ba, a gun taron.

A takaice dai, za a iya cewa, taron na birnin Munich yana alamta irin halin da dangataka tsakanin Jamus da Amirka ke ciki ne a halin yanzu. An dai sami sassaucin tsamari tsakanin bnagarorin biyu, amma barakar bambancin ra'ayin da ta raba su, har ila yau tana nan kamar yadda take a da.