1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Spain za ta dauki bakuncin taron COP25

Abdoulaye Mamane Amadou
November 1, 2019

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana kasar Spain a matsayin wadda za ta karbi bakuncin babban taro kan sauyin yanayi na COP25 wanda za a yi cikin watan Disamban da ke tafe.

Polen Kattowitz COP24 Klimakonferenz
Hoto: picture-alliance/AP Photo/C. Sokolowski

Gabannin fidda wannan matsayin da majalisar ta dauka dai kasar Chile ce aka tsara za ta dau nauyin taron sai dai ta sanar da janyewa daga daukar nauyinsa sakamakon jerin zanga-zanga da kasar ke fuskanta.

Taron dai zai gudana ne daga 2 zuwa 13 ga watan na gobe idan Allah ya kaimu, inda kwararru da shugabannin kasashe za su yi musayar yawu kan matsalar sauyin yanayi da hanyoyin da za a bi wajen magance matsalar.