1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron PDP a Najeriya ya zaɓi Jonathan

January 14, 2011

Bisa ga tarihin zaɓe a Najeriya tun bayan shekara ta 1999, Goodluck Jonathan na da kyakkyawar damar lashe zaɓen shugaban ƙasa a watan Afrilu da ke tafe.

Shugaba Jonathan mutumin da PDP ta tsayar a matsayin wanda zai yi mata takara a zaɓe mai zuwaHoto: AP

Da gagarumin rinjaye shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya lashe zaɓen tsayar da ɗan takarar jam'iyar PDP mai mulki. Daga cikin jihohin da suka jefa masa ƙuri'u har da na arewacin ƙasar inda musulmai ke da rinjaye. Zaɓen na Jonathan a matsayin ɗan takarar neman shugabancin Najeriya ƙarƙashin inuwar jam'iyar PDP, ya ba shi matsayin mai ƙarfi da zai kai shi ga lashe zaɓen shugaban ƙasa da aka shirya gudanarwa a ranar tara ga watan Afrilu da ke tafe, kasancewar PDP ɗin ce ta yi ta lashe zaɓuka a ƙasar tun bayan da ta koma kan turbar demokuraɗiyya a shekarar ta 1999. Jonathan ya samu yawan ƙuri'u 2736 yayin da Atiku Abubakar wanda ya taɓa riƙe muƙamin mataimakin shugaban ƙasa, ya samu ƙuri'u 805. Atiku Abubakar hanshaƙin ɗan kasuwa daga arewacin Najeriya, ya yi fatan samun gagarumin goyon baya a arewacin ƙasar yankin da ya fito.

Tsayawar Jonathan takarar dai ta zo da gadardama saboda yarjejeniyar tsarin karɓa-karɓa a tsakanin 'ya'yan jam'iyar ta PDP, inda za a yi ta zagayawa da shugabanci, tsakanin arewaci da kudancin ƙasar bayan wa'adin shugabanci sau biyu. Jonathan ɗan yankin Niger Delta mai arzikin man fetir, ya gaji shugabanci ne daga marigayi Umar 'Yar'Adua, wanda ya rasu a bara lokacin wa'adin mulkinsa na farko.

A ƙasa kuna iya sauraron rahotannin da wakilanmu a Abuja Ubale Musa da Uwais Abubakar Idriss suka aiko mana game da tsayar da Jonathan ɗin.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Usman Shehu Usman