1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

TARON SHEKARA SHEKARA NA BANKIN DUNIYA DA IMF.

October 6, 2004

Babban Bankin duniya da IMF sun kammala taron dasuka gudanar a karshen mako a birnin Washinton,ba tare da wani sakamakon kirki wa kasashe masu tasowa ba,sai dai bisa dukkan alamu mahalarta sun mikawa kasashe masu arzikin masanaantu matsalolin basussuka da ake bin kasashe matalauta.

Shugaban Bankin Duniya,James Wolfensohn.
Shugaban Bankin Duniya,James Wolfensohn.Hoto: AP

Taron na shekara shekara ya tabo muhimman batutuwa da dama,inda wasu kasashe masu tasowa suka nemi a cewa a basu karin daman tofa albarkacin bakinsu tare da wakilci na sosai da sosai cikin harkokin masanaantun kudin biyu na duniya,dake da matsaugunai a birnin Washinton,sai dai wannan bukata tasu bata samu martani daga jamian Bankin duniya da hukumar bada Lamuni ta IMF din ba.

Jamian kazalika sun tattauna daukan nauyin ayyukan tarzoma,tattalin arziki na duniya da kuma farashin mai.Amma batu da aka fi mayar da hankali a akai shine yafe basussukan da ake bin kasashe matalauta 100 bisa 100.Ministocin kudi daga kungiyar kasashe masu arzikin masanaantu na G7,wadanda keda madafan iko a masanaantun kudin biyu,tun a ranar Jummaa suka kammala ganawarsu ba tare da sun cimma wani tudun dafawa kann batun soke basussukan da ake bin kasashe matalautan ba,sai dai abu guda shine batun ya samu goyon baya daga kasashe dake fada aji a harkokin na kudi na duniya da suka hadar da Amurka da Britania.

Shi kuwa Directan hukumar ta IMF Rodrigo de Rato ya bayyana taron na wannan shekara da kasancewa babban nasara,dangane da muhimman batutuwa da aka tattauna,da suka hadar da hanyoyi da zaayi rangwame wajen biyan bashi,sai dai ya fadawa yan jarida cewa babu wani sakamako da aka cimma.

Shi kuwa Shugaban bankin duniya James Wolfensohn ya danganta dalilan da suka haifar da rashin cimma wani sakamako da karancin daidaito na siyasa a a bangaren kasashe masu hannun jari.Yace dole ne su marawa wadannan kasashe baya,sai dai yayi fatan cewa zaa samu warware matsalar ba tare da wata matsala ba,nan bada jimawa ba.

Sai dai rashin haifar da da mai idanu kann batun basussukan na kasashe matalauta ya muzantawa kwararru ta fannin tattali da kungiyoyi masu zaman kansu da suka halarci wannan taro

Daga cikin Kasashe 41 da bankin duniya ya jera a matsayin wadanda ake bin bashi,33 na daga nahiyar Afrika ,wadanda ake binsu bashin kimanin dala billion 220.Wanda ke nuni dacewa kowane yaro da aka haifa ko kuma zaa haifa a Nicaragua,nada bashin kimanin dala 2,000,akasar da a kowace shekara magidanci na kashe dala 390 kachal kann kayayyakin masarufi.

Manazarta sun zargi jamian turai da Amurka na kin daukan wani mataki lokaci mai tsawo daya gabataAna dai zargin sashin maaji na Amurka da soke yunkurin yafewa kasashe matalautan basussuka da ake binsu,tare da maye gurbin bashi da tallafi wa irin wadannan kasashen.

Tuni dai wasu kungiyoyi dasukayi nazari kann wannan taro na bankin duniya da IMF ,suka gabatar da sanarwa a wannan makon ,inda suka soki taron da gazawa wajen cimma wani sakamako dangane da matsaloli na basussukan da ake bin kasashe.Kungiyoyin sunyi nuni dacewa,Kasar Iraki da ake bin bashin dala Billion 120 yafi daukan hankali,fiye da sauran kasashe matalauta,wadanda kuma suka tara wadannan basussuka a makamancin mulkin kama karya na tsohon shugaba Sadam Hussein.Amurka ta nemi kasashe masu arzikin masanaantu su yafewa Iraki kashi 95 daga 100 na basussukan da ake binta,kasar da har yanzu dakarun Amurkan ke mamaye.Kasashen Faransa,Jamus da rasha,wadanda sune kebin Irakin kudi mafi yawa,sun bayyana muradin amincewa yafe kashi 50 ne kadai daga cikin 100.

Zainab Mohammed.