1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron shugabanin Afurka kan tsaro

February 18, 2012

Shugabanin Afurka na gudanar da taro a Jamhoriyar Bini domin daukar matakin bai daya dangane da tashe-tashen hankulan da suka addabi yankin.

Der Präsident von Benin, Thomas Boni Yayi, spricht am Sonntag (04.11.2007) im Kloster Eberbach bei Eltville bei einer Pressekonferenz. Bundespräsident Köhler hatte zur dritten von ihm veranstaltete Afrika-Konferenz unter dem Titel "Herausforderungen des Wandels - afrikanische und deutsche Antworten" geladen. Foto: Frank Rumpenhorst dpa/lhe +++(c) dpa - Report+++
Thomas Boni Yayi shugaban kasar Bini kuma sabon jagorar kungiyar Tarayyar AfurkaHoto: picture-alliance/ dpa

Shuwagabanin Afurka suna gudanar da tattaunawa dangane da rashin tsaron da ake fama da shi a yankin Sahel, inda sabon rikici ya barke a arewacin Mali, abun da masu fafutukar kare hakkin dan adam suka kwatanta a matsayin wani matasannacin bala'i, wanda ya addabi yankin a karon farko bayan shekaru 20. Shugabani 25 aka sa ran zasu halarci taron wanda ke gudana a Jamhoriyar Bene. Ministan harkokin wajen kasar Nasiru Arifari Bako, ya fadawa kmafanin dillancin labarun Faransa wato AFP cewa makasudin taron dai shine hada kan shugabanin ta yadda zasu tunkari matsalolin da ke addaban yankunan nasu da mataki na bai daya.

Wannan na zaman taron farko na Kungiyar Tarayyar Afurka, wanda shugaba Thomas Boni Yayi yake jagoranta tun bayan da ya zama shugaban kungiyar a watar da ta shige.

An dai kashe mutane da dama a yayinda dubai kuma suka kaurace, zuwa kasashe daban daban tun bayan da yan tawayen abzinawa suka kai hari a arewacin Mali. Kwamitin kasa da kasa ta Red Cross ko kuma Croix Rouge ta ce akalla mutane dubu 60 suka rasa matsugunnen su a cikin Mali a yayin da wasu dubu 44 kuma suka tsere zuwa neman mafaka a kasashe makota irinsu Burkina Faso, Mauritania da Nijar.

Mawallafiya: Pinado Abdu-Waba
Edita: Umaru Aliyu