1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron shugabannin Larabawa akan Siriya

March 28, 2012

Ana ci gaba da samun saɓani a tsakanin shugabannin Larabawa game da hanyar warware rikicin Siriya a yayin da Iraƙi ke karɓar baƙuncin taron su.

Arab Foreign ministers meet in Baghdad, Iraq, Wednesday, March, 28, 2012. Foreign ministers of the 22-member Arab League meeting in Baghdad will ask their heads of state to urge the Syrian regime to halt its crackdown on civilians and allow humanitarian groups into the country. (Foto:Karim Kadim/AP/dapd)
Taron ministocin waje na kasashen Larabawa a IrakiHoto: dapd

Gabannin taron da shugabannin ƙasashen Larabawar ke farawa a wannan Alhamis dai, ministocin kula da harkokin ƙetare na ƙasashen ƙungiyar sun yi taron share fage a birnin na Bagadaza amma suka gaza cimma daidaito akan hanyar kawo ƙarshen zubar da jini a ƙasar Siriya, da neman gwamnatin ƙasar ta dakatar da farmakin da take kaiwa akan fararen hula, game da baiwa ƙungiyoyin agaji damar kaiwa jama'a ɗauki da kuma sakin fursunonin siyasa, amma kuma taron ministocin zai gabatar da shawarwarin sa akan batutuwan ga shugabannin ƙasashen Larabawar domin ganin irin matsayin da za su ɗauka a lokacin taron su na yini biyu.

Sai dai kuma tunma gabannin taron ne wani kakakin ma'aikatar kula da harkokin wajen Siriya Jihad Makdessi ya ce Siriya ba za ta mutunta duk wata shawarar da ƙungiyar ƙasashen Larabawa mai mambobi 22 za ta yanke ba.

Saɓanin dake ci gaba da wanzuwa a tsakanin ƙungiyar Larabawar game da irin matakin da za ta ɗauka akan Siriya ya sa manazarta na cewar wani tabbaci ne ga salon ƙungiyar na kasancewar ta 'yan mulkin kama karyar dake neman biyan buƙatun kawunan su na siyasa amma ba wai na wanzar da tafarkin dimoƙraɗiyya a yankin ba, kuma hakan bai baiwa kowa mamaki ba, kama daga yammaci har zuwa gabashin duniya.

Ko da shike ƙungiyar ce ta nemi sanya takunkumin daya kai ga hamɓarar da gwamnatin Libiya dama kissar tsohon shugaban ta Mouamer Gadhafi, amma a yanzu hatta ita kanta ƙasar Iraƙi mai masaƙin baƙin shugabannin Larabawar ba ta goyo bayan sauyin gwamnati a ƙasar Siriya. A cewar Farfesa Hamadi al-Aouni, ƙwararre a sha'anin yankin Gabas Ta Tsakiya dake jami'ar birnin Berlin na Jamus, hatta ƙasashen dake sahun farko wajen neman sanyawa Siriya takunkumi bisa gallazawa 'yan fafutukar neman dimoƙraɗiyya a ƙasar kamar su Saudiyya da Qatar, buƙatun su na siyasa ne kawai suka sanya a gaba, dubi da yanda lanmura ke tafiya a cikin ƙasashen su:

" Ya ce, Ƙasashen dai ba sa bin dimoƙraɗiyya a cikin gida, kai ba su ma da majalisun dokoki, kuma da wuya suke mutunta haƙƙin bil'Adama, amma kuma wai waɗannan ƙasashen ne ke son ganin duniya ta amince da su game da ƙaunar an wanzar da tsarin dimoƙraɗiyya a wasu wuraren. A taƙaice dai wannan baya bisa tsari."

Dama dai anyi amannar cewar ƙasashen Saudiyya da Qatar dake yankin tekun Fasha na son samarwa 'yan adawar Siriya makamai domin tinƙarar gwamnatin ƙasar su da kuma shata wani yanki a cikin Siriya inda zai kasance tudun mun tsira ga 'yan adawar kana inda za su gudanar da harkokin su ba tare da wata tsangwama ba, amma kuma kamar yadda Elham Manea ta jami'ar Zürich tace suna tsangwamar 'yan adawa a cikin gida:

"Ta ce muna ganin ƙasashe biyu Saudiyya da Qatar waɗanda sam sam ba sa bin dimoƙraɗiyya amma kuma suna fakewa da batun mutunta 'yancin jama'a wajen neman wasu ƙasashe su biya buƙatun al'ummomin su, wanda ko da shike ya halatta a hannu guda, amma a ɗaya hannun Saudiyya na farma 'yan Shi'a dake yankin gabashin ƙasar ta, waɗanda ke yin boren neman sauyi a kullu yaumin. Anan za mu ga cewar akwai rashin nagarta. Ba na ganin Saudiyya da Qatar suna neman biyan buƙatun siyasar su bisa ingantattun dalilai."

Burin da ƙasashen biyu dama wasu ƙawayensu a yankin tekun na Fasha ke son cimma shi ne rage ƙarfin faɗa a jin da Iran ke da shi a Siriya a ƙarƙashin gwamnatin shugaba Bashar al-Assad, amma kuma gwamnatin Iraƙi wadda mabiya Shia'a ke shugabanta ta ce ba ta goyon bayan sauyin shugabanci a Siriya.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Yahouza Sadissou