Kasashen Larabawa na nazarin tsadar rayuwa
November 2, 2022Taron na zuwa ne a daidai lokacin da tattalin arzikin duniya ke cikin wadi-na-tsaka-mai wuya da hauhawan farashi da kuma karancin abinci da makamashi, daura da fari da tsadar rayuwa da ke addabar kasashen yankin Gabas ta Tsakiya da Afirka.
Sarakuna da shugabannin kasashe da fraministocin, na nazarin batutuwa da suka hada da sake maido da dangantakar diplomasiyya tsakanin Izra'ila da kasashen Larabawa hudu, a daidai lokacin da tsohon framinista Benjamin Netanyahu da 'yan jam'iyyarsa ke shirin sake kama madafan iko bayan nasara a zaben kasar.
Masar da Lebanon da Tunisiya na daga cikin kasashen Larabawa da radadin yakin Rasha da Ukraine ya fi gasawa tsakuwa a hannu, kuma a yanzu ke fafutukar sayen alkama da makamashi daga ketare domin wadata al'ummarsu.