Taron sulhu tsakanin Armenian da Azerbaijan
February 28, 2024![Jamus na tattauna sulhu tsakanin Armenia da Azerbaijan](https://static.dw.com/image/68398463_800.webp)
Talla
Jamus ta karbi bakuncin taron ne da nufin sulhunta rikicin da ke tsakanin kasashen biyu makobtan juna da suka shafe gomman shekaru suna zaman tankiya.
Taron na zuwa ne bayan ganawa tsakanin shugabannin kasashen biyu a daura da taron tsaro na duniya da ya gudana a birnin Munich na Jamus a farkon watan Fabrairu. A watan Disdambar bara kasashen biyu sun fidda sanarwa da suka ce suna bukatar cimma yarjejeniyar zaman lafiya a tsakaninsu.
Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz ya shiga tsakani a tattaunawar ta Munich inda Firaministan Armenia Nikol Pashinyan da shugaban Azerbaijan Ilham Aliyev suka amince su ci gaba da tattaunawar sulhu.