Taron sulhunta rikicin siyasar Togo
May 28, 2006Talla
Wakilin mussamman na Majalisar Sinkin Dunia mai kulla da yankin yammacin Afrika, na ci gaba da tantanawa, da ɓangarori daban daban na ƙasar Togo, da zumar samar da masalaha, a rikicin siyasar wannan ƙasa.
Ahmedou Ould Abdallah, ya sauka juma´ar da ta wuce a birnin Lome.
Tun ranar 21 ga watan da ga ya gabata, yan siyasar Togo, su ka koma tebrin shawara, domin cimma daidaito a kan wani daftari, da zai samu amincewar ɓangarori masu gaba da juna.
A yanzu haka, ƙiddidigar hukumar Majalisar Ɗinkin Dunia mai kulla da yan gudun hijira, ta nunar da cewa, akwai a ƙalla yan gudun hijira na ƙasar Togo, kimanin dubu 20, da ke zaune a Benin, sakamakon rikicin siyasa, da ya wakana ƙasar, a watan Aprul na shekara bara.