1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ganawar tattalin arziki tsakanin Turai da Afirka

Mouhamadou Awal Balarabe SB/LMJ
November 20, 2023

Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz ya karbi bakuncin takwarorinsa na kasashen Afirka fiye da goma, a taron hadin gwiwa tsakanin Jamus da Afirka da ke da nufin janyo hankalin masu zuwa jari zuwa Afirka.

Birnin Berlin na Jamus | Firaminista Abiy Ahmed Ali na Habasha da Olaf Scholz Shugaban gwamnatin Jamus
Firaminista Abiy Ahmed Ali na Habasha da Olaf Scholz Shugaban gwamnatin JamusHoto: Fabrizio Bensch/REUTERS

Shugabannin siyasa daga Afirka da Turai suna sake ganawa a birnin Berlin na Jamus don fadada yarjejeniyar da aka kulla tsakaninsu a shekarun baya. Manufar da aka sa a gaba ita ce zuba jari na kanfanoni masu zaman kansu a nahiyar Afirka. Amma kuma har yanzu da sauran tafiya idan aka yi waiwaya ci gaban da shirin "Compact with Africa" ya samar a nahiyar Afirka.

Kafrin Bayani: Jamus na son karin masana'antu a Afirka

Alkiblar da aka sa a gaba dai a bayyane take: kasashen Afirka da na Turai na son yin aiki kafada da kafada da nufin da ba da kwarin gwiwa ga masu zuba jari masu zaman kansu. Saboda haka ne shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz ya gayyaci shugabannin kasashen Afirka da dama da 'yan siyasa dominhalartar taron tattalin arziki na "Compact with Africa" a Berlin babban birnin tarayyar Jamus. Baya ga mai masaukin baki Olaf Scholz da ministan tattalin Arzikin Jamus Robert Habeck, akwai shugabar hukumar zartaswa ta KungiyarTarayyar Turai Ursula von der Leyen da Shugaban Faransa Emmanuel Macron da shugabannin kasashen Afirka 10 da kuma ministoci fiye da 30 daga Afirka da ke hallara a Berlin.

Taro kan Afirka a birnin Berlin na JamusHoto: Michele Tantussi/AFP/Getty Images

Tsohuwar shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ce kafa shirin "compact witf Africa" a lokacin da kasarta ta jagoranci kungiyar G20 ta kasashen da ke da karfin masana'antu a duniya. ko da  Heiko Schwiderowski, shugaban sashen kudu da hamadar Sahara na Afirka a cibiyar kasuwanci da masana'antu ta Jamus (DIHK) sai da ya jaddada cewa, wannan taro na zuba jari da ya kunshi mahalarta 800 ya kasance taron tattalin arziki mafi girma da aka taba gudanarwa a kasar Jamus da nufin aike da wata alama mai mahimmanci ga nahiyar Afirka.

Compact with Africa (CwA) na dogara kacokan kan kyakkyawan shugabanci da tsarin gyaran fuska ga wasu dokokin da suka shafi kasuwanci a yawancin kasashen Afirka. Ya zuwa yanzu dai, kasashe 13 na Afirka ne suka rungumi wannan shiri ciki har da Jamhuriyar Benin da Burkina Faso da Côte d' Ivoire da Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kwango da Masar da Habasha da Ghana da Guinea da Maroko da Ruwanda da Senegal da Togo da Tunisiya. Duk da cewa Afirka ta Kudu, daya daga cikin manyan kasashen Afirka da ke da karfin tattalin arziki ce ke jagoranci taron a wannan karon, amma an gayyaci wasu kasashe kamar Angola da Zambiya da Najeriya da Kenya da suka halarta.

Ga masanin tattalin arziki na kasar Ghana Emmanuel Bensah, tabbas "Compact with Africa" wani tsari ne mai mahimmanci don auna irin ci-gaban tattalin arzikin nahiyar Afirka da kuma abin da ya kamata a inganta. Amma kuma akwai masana tattalin arziki na Jamus irin su Robert Kappel da ba su da kwarin gwiwa game ga makomar "Compact  with Africa" saboda ya fara nuna alamun tafiyar hawainiya, yana mai cewa yawancin jarin ana zuba su ne a fannin makamashi da albarkatun karkashin kasa na afirka, saboda haka akwai bukatar mayar da hankali a fannin abubuwan more rayuwa.