1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron tattaunawa a Maroko

May 18, 2011

Gidauniyar Bertelsmann ta nan Jamus tana zaman wani muhimmin dandalin tattaunawa da neman kusantar juna tsakanin ƙasa da ƙasa

Ministan harkokin wajen Jamus Guido Westerwelle a Marakesh ta ƙasar MarokoHoto: picture-alliance/dpa

A halin da ake ciki yanzu haka a haɗin guiwa da ma'aikatar harkokin wajen ƙasar Maroko, gidauniyar ta shirya wani taron ƙwararrun domin nazarin canje-canjen da ake samu a ƙasashen arewacin Afirka. Ministan harkokin wajen Jamus Guido Westerwelle dake ziyarar ƙasar ta Maroko na daga cikin waɗanda suka halarci taron a birnin Rabat.

An dai sha ji daga bakin ministan harkokin wajen Jamus Guido Westerwelle yana mai kwatanta guguwar canjin dake kaɗawa a arewacin Afirka, kama daga Tunesiya zuwa sauran sassa na yankin, tamkar wani ci gaba na tarihi.

An dai lura da sararawa a fiskar ministan harkokin wajen na Jamus a ziyararsa ga ƙasar Maroko, lamarin dake nuna gamsuwarsa da ci gaban da ake samu a yankin na Maghreb, musamman ma ganin cewar maganar ba ta shafi wata matsala ce ta jam'iyyar Free Demokrats ko tura sojoji zuwa Libiya ba, abu ne da ya shafi wata manufa ta juyin-juya-hali a ƙasashen Larabawa:

Dubban masu zanga-zangar neman sauyi a Rabat ta MarokoHoto: DW

"Jamus ta amsa kiran neman walwala da jama'a ke yi kuma muna nan daran daƙau a bayan masu fafutukar neman demokraɗiya. Al'umar ƙasashen arewacin Afirka da na yankin gabas ta tsakiya su ne suka ta da ƙurar guduwar ta canji."

Jamus na da cikakkiyar azama ta ba da goyan baya ga ƙasashen dake fafutukar kawo canji ga al'amuransu, musamman ma dai ƙasashen Tunesiya da Masar da kuma Maroko, akan hanyarsu ta girka demokraɗiyya tsantsa. To sai dai kuma shi kansa Westerwelle na sane da cewar girka demokraɗiya kawai ba zai wadatar ba. A saboda haka ma'aikatar harkokin wajen Jamus ta ware tsabar kuɗi Euro miliyan hamsin daga baitul-malinta don tallafa wa al'amuran shari'a da dangantakar jami'o'i da nagartattun hanyoyin samar da makamashi a ƙasashen arewacin Afirka. Amma abu mafi muhimmanci a baya ga dangantakar ƙasa da ƙasa, wajibi ne ita kuma ƙungiyar tarayyar Turai ta bayyana alƙiblar da ta fiskanta bisa manufa in ji ministan harkokin wajen Jamus Guido Westerwelle:

"Wajibi ne illahirin al'uma a ƙasashen da guguwar canjin ke kaɗawa su fara gani a ƙasa, saboda babu wata dama ta sake maido da hannun agogo baya dangane da wannan ci gaba da ake samu. Ta la'akari da haka ya zama wajibi ƙasashen Turai su fara buɗe ƙofofin kasuwanninsu ga abubuwan da ƙasashen na arewacin Afirka, masu fafutukar girka mulkin demokraɗiyya, ke sarrafawa."

Harin ta'addanci a Marakesh a ƙarshen watan da ya gabataHoto: dapd

Wani muhimmin abu ga Westerwelle kuma shi ne kasancewar ƙasar Maroko ta dage akan hanyar da ta durfafa duk da harin ta'addancin nan da aka kai a birnin Marakesh a ƙarshen watan afrilun da ya gabata. Hakan na ma'ana ne cewar tsarin mulkin demokraɗiya da addinin musulunci na tafiya ne kafaɗa-da-kafaɗa da juna. A saboda haka a yanzu lokaci yayi da ƙasashen Turai zasu canza salon tunaninsu a manufofinsu dangane da maƙobtansu na arewacin Afirka domin cuɗe-ni-in-cuɗe-ka da juna:

"Ƙasashen na arewacin Afirka na maƙobtaka ne kai tsaye da nahiyar Turai, a saboda haka kwanciyar hankali da zaman lafiyar waɗannan ƙasashe ke da muhimmanci ga nahiyar."

Mawallafi: Alexander Göbel/Ahmad Tijani Lawal

Edita: Mohammed Nasiru Awal