Taro zai taimaka wajen magance matsalolin tsaro?
February 12, 2026
Shugabannin Turai sun kasance cikin halin shakku maimakon fata na gari, gabanin taron tsaron Munich daga 13 zuwa 15 ga Fabrairun 2026, saboda dangantaka tsakaninsu da Shugaba Donald Trump ta tabarbare shekara guda bayan dawowarsa kan kujerar mulki. Hasali ma dai, manufofin harkokin wajen na Trump na jefa shakku kan babban taron na duniya (MSC).
A tsawon shekaru da dama, taron ya ayyana kansa a matsayin na kasashen yammacin duniya. Amma a yanzu, kamar yadda shugabanta Wolfgang Ischinger ya fada, akwai "rashin yarda da aminci da ba a taba gani ba" a karkashin rahotonsa mai taken " a kan hanyar rushewa". Rahoton ya danganta Donald Trump da daya daga cikin shugabannin da ke karar tsaye ga dokoki da cibiyoyin duniya masu daraja. Kalaman Trump na cewa baya bukatar dokokin kasa da kasa na daya daga cikin misalai da yawa a wannan marra.
Ko da yake yanayin diflomasiyya na fuskantar kalubale fiye da baya, amma taron tsaro na Munich da aka kafa sama da shekaru 60 da suka gabata, ya kasance wani dandali na musayar ra'ayi da tattaunawa kan tsaro. Kuma daga cikin mahalarta sama da 1,000, akwai wakilan gwamnati sama da 200 daga kasashe 120. Wadanda ake sa ran za su halarta sun hada da Shugaban Ukraine Volodymyr Zelenskyy, Shugaban Faransa Emmanuel Macron, ministan harkokin wajen China Wang Yi, da firayiministar Denmark Mette Frederikse.
Duk da tabarbarewar dangantakar da ke tsakanin kasashen Yamma, wata babbar tawaga daga Amurka za ta sake halarta a wannan shekarar, inda sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio zai wakilci gwamnatin Trump. Ana sa ran Rubio zai "yi magana kan manufofin harkokin wajen Amurka amma ba game da batutuwan da ba su shafi ma'aikatarsa kai tsaye ba. Amma tawagar Amurka ba ta kunshi magoya bayan Trump kawai ba, inda ta kunshi masu adawa da shi kamar Gavin Newsom, gwamnan California.
Sabanin shekarun baya, ba a maraba da wakilan gwamnatin Iran a Munich a wannan shekarar, sakamakon amfani da karfi da suka yi wajen dakile mummunar zanga-zanga kan tsadar rayuwa. Amma ana san ran wakilan 'yan adawa da kungiyoyin fararen hula za su yi jawabi a taron tsaro na Munich.
Sannan duk da cewar yakin da Rasha ke yi da Ukraine zai sake zama babban jigo, amma wakilan gwamnatin Rasha ba za su kasance a Munich ba. ko da a shekarar 2022, jim kadan kafin Rasha ta mamaye Ukraine, tawagar Rasha ta fice daga taron gaba daya, inda tun daga lokacin, ba a sake jin duruyarta ba.
Dangane da yiwuwar kawo karshen yakin kuwa, Ischinger da ke zama shugaban taron MSC ya jaddada cewa yayin da Rasha ke nuna alamar son tattaunawa, a lokaci guda kuma tana jefa rayuwar fararen hular Ukraine cikin mawuyacin hali. Saboda haka ne ba za a ba da kyautar Ewald von Kleist ta MSC ga mutum da ya fi cancanta a wannan shekarar ba, amma dai "al'ummar Ukraine saboda karfin halinsu."
A daya hannun kuma, an sake gayyatar 'yan siyasa na AfD mai kyamar baki a Jamus bayan mayar da ita saniyar ware na tsawon shekaru biyu. An gayyaci kusoshin jam'iyyar AfD guda uku daga Bundestag, amma ba za su yi wani jawabi ba.