Taron Turai da Afirka a Libya
November 28, 2010Ministan kula da harkokin wajen Libya Moussa Koussa ya sanar da cewar, shugaban ƙasar Sudan Umar al-Bashir baya cikin jerin shugabannin Afirkar da za su halarci taron haɗin gwiwa a tsakanin Tarayyar Turai da kuma Tarayyar Afirkar da zai gudana - farawa daga wannan Litinin ba. A maimakon haka - a cewar ministan, shugaba al-Bashir zai halarci taron kwamitin sulhu da samar da zaman lafiya na ƙungiyar Tarayyar Afirka ne.
Ya ce hukumomin Libya sun buƙaci shugaban na Sudan daya ƙauracewa taron ne saboda barazanar da shugabannin Turai suka yi na janyewa daga taron - idan har ya halarta, inda ministan harkokin wajen Libyar ya ce ƙasar sa ta yi namijin ƙoƙari wajen karɓar baƙuncin taron, kuma ba ta son janyo wani cikas ta hanyar ficewar wasu shugabanni daga zauren taron.
Idan za'a iya tunawa dai kotun ƙasa da ƙasa da ke hukunta masu aikata manyan laifukan yaƙi ne ta bayar da sammacin kame shugaba Umar al-Bashir bisa zargin aikata kissar ƙare dangi a yankin Darfur.
Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Abdullahi Tanko Bala