1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

MDD da Jamus za su jagoranci taro kan Libiya

Zainab Mohammed Abubakar
October 5, 2020

A yunkurin baya baya bayan nan na warware ricikin Libiya, Majalisar Dinkin Duniya da Jamus za su dauki nauyin gudanar taro domin tattauna halin da kasar ke ciki.

Libyen-Ägypten-Waffenruhe
Hoto: Getty Images/AFP/M. Turkia

Taron da zai gudana ta kafar bidiyo, zai samu halartar babban sakataren MDD Antonio Guterres da ministan harkokin wajen Jamus Heiko Maas, wanda ke zuwa bayan wanda ya gudana a birnin Berlin cikin wannan shekara.

Ana sa ran kasashe 16 da kungiyoyin kasa da kasa da suka halarci taron na Jamus a baya, za su kasance a taron na wannan rana ta Litinin, a kokarin da ake yi na gano bakin zaren warware rikicin kasar ta Libiya.