1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron 'yan majalisun nahiyar Afirka a Abuja

November 12, 2013

'Yan majalisa daga sassa daban-daban na Afirka na taro a Abuja da nufin nazarin mafita bisa tsarin da ya fifita bangaren zartarwa bisa majalisun dokoki a cikin nahiyar

Description en:House of Representatives of Nigeria Date 16 September 2005, 11:13 Source The House of Representatives Author Shiraz Chakera ou are free: to share – to copy, distribute and transmit the work to remix – to adapt the work Under the following conditions: attribution – You must attribute the work in the manner specified by the author or licensor (but not in any way that suggests that they endorse you or your use of the work). share alike – If you alter, transform, or build upon this work, you may distribute the resulting work only under the same or similar license to this one.
Hoto: cc-by-sa/Shiraz Chakera

A wani abun dake zaman sabon yunkurin su na kwato 'yanci da nufin aiyyuka na cigaba, 'yan majalisu daga sassa daban daban na nahiyar Afirka na can na taro a Abuja da nufin nazarin mafita bisa tsarin da ya fifita bangaren zartarwa bisa majalisun dokoki a cikin nahiyar

An dai dauki tsawon lokaci ana karatu na demokaradiya dama amfaninta tsakanin al'umma, an kuma share tsawon lokaci ana jiran gawo irin na shanu a tsakanin al'ummar da ake ci da guminsu dominsu sakamakon gazawar da ake dangantawa da aiyyukan majalisun dokokin kasashen, da kundin tsarin na demokaradiya ya dorawa alhakin dokoki na cigaban al'uma

Abun kuma da daga dukkan alamu ya fara jawo tari na damuwa a tsakanin 'yan majalisu na nahiyar da suka taru anan Abuja da nufin nazarin mafita ga batun na tabbatar da 'yanci na aiyyukan majalisun ba tare da tsoma baki na bangaren zartarwa a cikin nahiyar ba.

Majalisar dokokin NajeriyaHoto: AP

Ra'ayoyi mabanbanta a taron

Duk da cewar dai ra'ayi ya zo daya a game da gazawar yan majalisun na sauke nauyin nasu, amma kuma an sha banban a tsakanin mahalartan sa dake kallon matsalar na da ruwa da tsaki daga amshin shatan da ake zargin 'yan majalisar da komawa bangaren zartarwar ya zuwa na rashin imanin masu mulkin kasashen nahiyar bisa yanci na cin gashin kan yan majlisun.

To sai dai kuma a fadar Atiku Abubakar dake zaman tsohon mataimakin shugaban tarrayar najeriya kuma daya a cikin masu gabatar da kasidu a cikin taron dai wai mafita na ga tsayawar majalisun cikin matsayinsu.

Tsayawa bisa aikin jama'a ko kuma kokari na wuce makadi cikin rawa dai ko a farkon wannan mako majalisar wakilan kasar ta zargi bangaren zartarwar da uwar watsi da kusan dokoki sama da 30 din da majalisar ta zauna ta amince kansu amma kuma shugaban kasar yace bai san da zamansu ba.

Majalisar dokokin MasarHoto: picture-alliance/AP Photo

Kyautata zaton cewa akwai burbushin soji

Abun kuma da a fadar Hon Alhassan Ado dake zaman dan majalisar wakilan Najeriyar kuma shugaban kungiyar yan majalisun dokokin nahiyar ta Africa can shirin raya kasar MDG ke nuna alamun har yanzu da burbushi na tunanin soja cikin zukatan shugabanni a cikin nahiyar.

Babiya Allah a cikin yanci ko kuma tabbatar da karfin iko na shugabanni dai taron na Abuja dake zaman irinsa na farko a tsakanin yan majalisun nahiyar a fadar Dr kabir mato dake zaman masani na sisyasa a nahiyar zai taimaka wajen fahimtar juna da imganta aiyuukan alumar nahiyar.

Abun jira a gani dai na zaman mafita a tsakanin yan majalisar dake neman hanyar yanci da kuma yan uwansu masu wukar yankan dake fadin da sauran tafiya.

Mawallafi: Ubale Musa
Edita: Pinado Abdu Waba